Hoton fim din Indiya na farko da aka yi da bakar fata mai suna 'Namaste Wahala' ya fita

Hoton fim din Indiya na farko da aka yi da bakar fata mai suna 'Namaste Wahala' ya fita

- Hamisha Daryani Ahuja 'yar asalin kasar India ce amma mazauniya Najeriya a jihar Legas

- Ta fada harkar fim inda ta shirya shaharren fim din da ya kunshi 'yan India da 'yan Najeriya

- Kamar yadda babbar 'yar kasuwar ta bayyana, fim din da ta shirya na kunshe da al'adun kasar India ne da na Najeriya

Hamisha Daryani Ahuja 'yar kasuwa ce a kasar India wacce ta koma sana'ar fim. Ta saki fim dinta na farko mai suna 'Namaste Wahala'.

'Namaste Wahala' fim ne wanda babu dadewa zai fito kuma ya samu umarnin Hamisha Daryani Ahuja ne, kamar yadda jaridar Pulse ta ruwaito.

'Yar kasar India amma mazauniyar jihar Legas din za ta fitar da fim din ne mai dauke da 'yan masana'antar Nollywood mai suna Ini Dima-Okoji.

Hoton fim din Indiya na farko da aka yi da bakar fata mai suna 'Namaste Wahala' ya fita
Hoton fim din Indiya na farko da aka yi da bakar fata mai suna 'Namaste Wahala' ya fita
Asali: Facebook

Hamisa ta bayyana a shafinta na Instagram a watan Janairu cewa za ta fada harkar fim tare da nuna yadda zai kasance. Ta ce zai taba al'adun kasar Indiya ne da na Najeriya.

KU KARANTA: Tashin hankali: Watana shida ina karanta Bible, kuma ina samun kwanciyar hankali idan na karanta - Fatima Yusuf

Ta wallafa "babu komai sai sha'awar hada fim na shiga masana'antar. Zan fitar da fim wanda zai bayyana al'adun kasar Indiya da na Najeriya. A lokacin da na fara wannan tunanin, na san akwai bukatar aiki tukuru tare da mayar da hankali sannan in ga hakan ta faru."

Kamar yadda jarumar fim din, Ini Dima-Okojie ta ce an kammala daukar fim din 'Namaste Wahala'. Hakan na nufin yana gab da fitowa kenan.

Sabon fim din ya kunshi taurari kamar Ajoke Silva da Richard Mofe Damijo. Akwai Broda Shaggi da mawaki MI Abaga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel