Kasar Saudiyya ta Haramta daukar hoto ko bidiyo a Masallacin Harami dana Annabi

Kasar Saudiyya ta Haramta daukar hoto ko bidiyo a Masallacin Harami dana Annabi

- A dai-dai lokacin da mutane suka mayar da daukar hoto a Masallacin Ka'aba dana Annabi tamkar ibada ko kuma muce al'ada

- An hankaltar da hukumomin kasar Saudiyya akan abinda ke faruwa, hakan ya sanya hukumar kasar sanya dokar hana daukar hoto a wadannan wurare guda

- Hukumar kasar ta baiwa jami'an tsaro damar kwace duk wani abu da aka ga anyi amfani dashi wajen daukar hoto a Masallatan guda biyu na birnin Makkah da Madina

A karshe dai gwamnatin kasar Saudiyya ta dauki mataki akan daukar hotuna da ake yi a Masallacin Ka’aba dana Annabi.

Miliyoyin mutane suna ziyartar kasar Saudiyya a kowacce shekara, kuma suna shafe tsawon lokacin da suka diba a can wajen ibada domin samun rahamar Allah. Suna kashe makudan kudade, amma kadan daga cikin mutane ne Allah ya basu ikon zuwa wannan waje.

Kasar Saudiyya ta Haramta daukar hoto ko bidiyo a Masallacin Harami dana Annabi
Kasar Saudiyya ta Haramta daukar hoto ko bidiyo a Masallacin Harami dana Annabi
Asali: Facebook

Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanya dokar daukar hoto da bidiyo ta hanyar amfani da kowacce na’ura a wadannan Masallatan guda biyu.

A yadda rahoto ya bayyana dokar an sanyata a kan Masallacin Annabi dake Madina, da kuma Masallacin Ka’aba dake birnin Makkah.

An bayyana cewa ministan kasar waje na Saudiyya shine ya sanar da sanya dokar ta hanyar aikawa jakadun kasar ta Saudiyya dake kasashen duniya wannan sako, inda mafi yawanci suka karbi wannan takarda a ranar 15 ga watan Nuwambar shekarar 2019.

Kasar ta saudiyya ta bayyana cewa ta dauki wannan mataki ne domin kare martabar wuraren ibadar, da kuma tabbatar da tsaro a lokacin da mutane ke gabatar da ibada.

KU KARANTA: Matashi dan asalin jihar Kano ya fito da fasahar koyon addinin Musulunci a waya

A ‘yan shekarun nan dai Mahajjata da yawa sunyi ta faman sanya hotunansu a shafukan sada zumunta na zamani kamar irinsu, Facebook, Instgram da Twitter, inda wasu zaka ga sun dauki hoton a gaban Ka’aba, ko kuma a cikin Masallacin Annabbi.

Wasu ma zaka ga sun dauki hoton a matsayin kungiya ne rike da tutar kasarsu a harabar Masallatan guda biyu. Mutane da yawa suna magana akan irin wadannan mutane shin suna zuwa ibada ne ko kuwa suna zuwa daukar hoto ne?

Yanzu haka dai gwamnatin kasar ta bawa jami’an tsaro damar kwace hoton ko kuma abinda aka yi amfani da shi aka dauki hoton ga duk wani wanda aka samu da karya wannan doka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel