Ina da yakinin cin hanci ne ya jawo Coronavirus - Magu

Ina da yakinin cin hanci ne ya jawo Coronavirus - Magu

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu, ya bayyana cewa yana da yakinin cewa cin hanci ne ya haddasa bullowar cutar coronavirus.

Magu ya bayyana hakan ne a wajen bikin yaye sabbin jami’an hukumar EFCC wanda aka gudanar a Kaduna.

Ya bayyana cewa cin hanci da rashawa ce babbar kalubalen bil adam sannan cewa sun kuma fi dukkanin cuta illa a duniya.

A cewarsa yaki da rashawa ba abu ne mai sauki ba, sannan cewa cin hanci ne ke kawo talauci, rashin aikin yi da kuma karancin ilimi da ababen more rayuwa marasa inganci.

Magu ya bayyana cewa a watanni shida da suka wuce, sun samu nasarar cafke sama da matasa 500 da ke zamba cikin aminci ta intanet kuma tuni aka maka su a kotu.

Ina da yakinin cin hanci ne ya jawo Coronavirus - Magu
Ina da yakinin cin hanci ne ya jawo Coronavirus - Magu
Asali: Facebook

Sai dai ya bayyana cewa baza su so a tura su gidan yari ba domin akwai wani shirin da suke kokarin yi da wasu hukumomi domin gyara rayuwar matasan.

Idan za ku tuna wannan annoba ta coronavirus ta halaka sama da mutane 1700 a duniya.

KU KARANTA KUMA: Diloli sun bayyana sirrin farin jinin dan tofi da rigar mama na gwanjo

A wani labari na daban, mun ji cewa Kwamishinan lafiya a jihar Kano, Dakta Aminu Tsanyawa, ya ce an kebe wasu mutane 70 a wata cibiya ta musamman domin basu kula wa ta musamman bayan an yi zargin cewa sun kamu da zazzabin 'Lassa'.

Tsanyawa ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin wata tattauna wa da manema labarai a wurin taron wayar da kai a kan zazzabin 'Lassa' a Kano.

Ya bayyana cewa an kebe wasu mutane 70 a wata cibiya ta musamman da gwamnatin jiha ta ware a Yar-Gayawa, yankin karamar hukumar Dawaki Kudu.

Dakta Tsanyawa ya kara da cewa gwamnati ta dauki matakan kiyaye wa tare da samar da kayan aiki, musamman a filin jirgin sama, domin duba lafiyar duk wanda suka Najeriya ta jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel