Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari Chibok, suna bankawa gidaje wuta

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari Chibok, suna bankawa gidaje wuta

Yan taa’ddan Boko Haram na kan kai hari yanzu a garin Korongilum dake karamar hukumar Chibok ta jihar Borno. The Cable ta ruwaito.

Wani mazaunin garin ya bayyanawa manema labarai cewa yan ta’addan sun shiga garin ne misalin karfe 6 na yamma kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

Hakazalika suna bankawa gidajen mutane wuta.

Yace “Dawowar mutane gida daga gonakinke da wuya, sai yan taaddan suka shigo. Sun samu shiga ne ta Forfor, kuma mutane na guduwa yanzu.“

Majiya daga gidan Soja yace dakarun Sojin 28 task force brigade and 117 battalion na hanyarsu ta zuwa Korongilum.

Yace “Lallai kwamandojin Brigade da Bataliyan ke jagorantan Sojojin.“

Ku saurari cikakken rahoton......

Asali: Legit.ng

Online view pixel