Yawan yi wa miji barazana da wuka: Kotu ta raba auren mata da miji

Yawan yi wa miji barazana da wuka: Kotu ta raba auren mata da miji

A ranar Talata ne wata kotun gargajiya da ke zamanta a yankin Igando, jihar Legas, ta amince da bukatar wani dan kasuwa, Daniel Abiodun, wanda ya nemi a raba aurensa da matarsa, Temitope, saboda yawan yi biyo shi da wuka zata illata shi duk lokacin da suka samu sabani.

Da yake raba auren, babban alkalin kotun, Adeniyi Koledoye, ya ce kotun bata da wani zabi da ya wuce ta raba ma'auratan saboda dagewar da mai kara ya yi duk da kotun ta yi kokarin shiga tsakani domin sulhunta su.

"Wannan kotu mai girma, bisa ikon da ta ke da shi, ta raba auren da ke tsakanin Mista Daniel Abiodun da matarsa, Temitope Abiodun, a wanann rana. Daga yanzu kun tash daga matsayin mata da miji.

"Kowannenku zan kama hanyarsa, ya ci gaba da rayuwarsa shi kadai, ba tare da tsangwamar juna ba. Wannan kotu tana mai yi muku fatan alheri a rayuwarku ta nan gaba," a cewar alkalin kotun.

Yawan yi wa miji barazana da wuka: Kotu ta raba auren mata da miji
Yawan yi wa miji barazana da wuka: Kotu ta raba auren mata da miji
Asali: UGC

Alkalin kotun ya dora wa Daniel alhakin ciyar da 'ya'yan da suka haifa, biya musu kudin makaranta da kula da lafiyarsu.

DUBA WANNAN: Dan Najeriya da aka yanke wa hukuncin kisa a kasar Saudiyya ya samu 'yanci

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa Daniel, dan kasuwa mai shekaru 56 a duniya, ya nufi kotun da bukatar neman ta raba aurensa da matarsa saboda tana barazanar cewa zata kashe shi.

A nata bangaren, Temitope, ta shaida wa kotun cewa Daniel yana yawan lakada mata duka kamar Jaka tare da rokon kotun kar ta amince da bukatarsa ta neman a raba aurensu. Sai dai, bukatarta bata samu karbu wa ba a gaban kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel