Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci bikin yaye sabbin jami’an EFCC a Kaduna

Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci bikin yaye sabbin jami’an EFCC a Kaduna

Shugaban kasa Muhaammadu Buhari ya kai ziyara jahar Kaduna domin halartar bikin yaye sabbin kananan jami’an hukumar EFCC, watau Detective Inspector Course karo na 5 a daya gudana a kwalejin horas da hafsoshin sojin Najeriya, NDA.

Bikin ya kawo karshen horo mai tsanani da jami’an suka samu a kwalejin NDA, wanda ake sa ran zai shirya sabbin jami’an don fuskantar kalubalen dake gabansu a harkar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

KU KARANTA: Majalisar wakilai ta bayar da kwangilar sayen motocin alfarma guda 400

Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci bikin yaye sabbin jami’an EFCC a Kaduna
Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

A cewar shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, EFCC ta hada kai da NDA ne domin horas da jami’an ta yadda ba zasu ji tsoron duk wani barazana da za’a musu a kan aikin yaki da rashawa ba, kuma ba zasu gajiya ba.

Da yake nasa jawabi a yayin biki, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sauye sauyen da suka gudanarwa a gwamnatinsa zasu kawar da duk wani kumbuya kumbuya da boye boye da ake yi a wajen harkar kudi a gwamnati.

“Burina shi ne na tabbatar da sauyi mai kyau wanda zai hana duk wasu masu burin rashawa sakat a cikin gwamnati, manufata shi ne na tabbata an gudanar da duk wasu cinikayyar gwamnati a bude, a bajeta a faifai, ta yadda jama’a zasu fahimci inda aka dosa.

“Mun dage kan lallai sai an hukumar yi ma kamfanoni rajista ta wallafa sunayen kamfanonin dake kasar nan tare da sunayen mamalakkansu, haka zalika ita ma hukumar hakar ma’adanan kasa za ta wallafa sunayen kamfanonin dake hake haken albarkatun kasa.

Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci bikin yaye sabbin jami’an EFCC a Kaduna
Jami'an EFCC
Asali: Facebook

“Na samu labarin an kammala gina shafin yanar gizon da za’a daura wadannan bayanai, amma har yanzu masu kamfanonin sun ki amincewa da sabon tsaro, toh da wannan nake kira a garesu dasu tabbata sun baiwa hukumomin da aikin ya rataya a kansu hadin kai.” Inji shi.

Daga karshe Buhari ya jinjina ma EFCC bisa kokarin da take yin a yaki da rashawa yadda ya kamata, don haka ya yanke cewa tabbas Najeriya na samun nasara a yakin da take yi da rashawa duba da tsare tsaren da EFCC ta sanya a gaba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng