Karya ne Buhari baya shirin zuwa hutu Birtaniya

Karya ne Buhari baya shirin zuwa hutu Birtaniya

Fadar shugaban kasa a ranar Litinin, 17 ga watan Fabrairu ta karyata labaran da ke yawo a kafofin sadarwa cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin zuwa hutu a kasar Birtaniya, Saudiya da kuma Astria.

A wata sanarwa da kakain shugaban kasar, Femi Adesina, ya fitar ta ce labaran na kanzon kurege ne kawai.

Ya kuma karyata rahotannin cewa Buhari ya zargi mazauna jahar Borno da hada kai da yan Boko Haram.

Karya ne Buhari baya shirin zuwa hutu Birtaniya
Karya ne Buhari baya shirin zuwa hutu Birtaniya
Asali: Twitter

“Wasu labaran karya na yawo a yanzu, kuma ana bukatar yan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan da irin abubuwan da suke ji a matsayin labarai, da kuma yada su zuwa ga sauran mutane musamman daga shafukan zumunta.

“Wani labara na ta yawo cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin tafiya Birtanbiyua na tsawon kwwanaki 20 sannan daga nan zai je Saudiya da kuma Austria. “Kanzon kurege ne. Ba komai bane face karya daga zukatan makirai."

Mista Adesina ya bukaci 'yan Najeriya da su kauracewa yada labaran karya.

A baya mun ji cewa fadar Shugaban kasa a ranar Lahadi, ta bayyana cewa ziyarar kwanan nan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai jahar Borno ya nuna cewa har yanzu yana da shahara da karbuwa, inda ta kara da cewa mazauna jahar sun yaba da abun da ya yi wajen magance ta!addanci a arewa maso gabas.

Shugaba Buhari ya ziyarci Maiduguri don yi masu jaje, biyo bayan hare-hare da yan ta’addan Boko Haram suka kai wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama a Audo da ke karamar hukumar Konduga na jahar Borno.

A yayin ziyarar, shugaba Buhari ya ziyarci Gwamnan Jahar, Babagana Zulum da Shehun Borno, Alhaji Abubakar El-Kanemi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da Kyaftin Nuhu a matsayin Shugaban NCAA

Hadimin Shugaban kasa na musamman a kafofin watsa labarai, Mista Femi Adesina, wanda ya bayyana a shirin Politics Today na Channels TV, ya ce dandazon jama’ar da suka tarbi shugaba Buhari na da matukar yawa sannan cewa yan tsirarun muryoyin da suka bijire ba abun damuwa bane.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel