Da duminsa daga kotun koli: An dage zaman sake duba shariar Imo zuwa watan gobe

Da duminsa daga kotun koli: An dage zaman sake duba shariar Imo zuwa watan gobe

Kotun Kolin Najeriya ta dage zaman sauraron bukatar sake duba shariar zaben gwamnan jihar Imo da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da tsohon gwamnan jihar Imo, Emeke Ihedioha, suka shigar.

Ihedioha ya bukaci kotun koli ta sake duba hukuncin da ta yanke na cireshi matsayin gwamnan jihar Imo.

Za ku tuna cewa Kotun kolin Najeriya da ta fititiki gwamnan PDP, Emeka Ihedioha, kuma ta baiwa na APC, Hope Uzodinma.

Yayinda aka shiga kotu da safen Talata, lauyan Ihedioha, Kanu Agabi SAN, ya bukaci kotun ta kara musu lokaci domin su tattara takardu da hujjojinsu, kuma lauyan APC da Hope Uzodinma, ya amince da hakan.

Kwamitin Alkalan kotun koli, karkashin jagorancin shugaban Alkalai, Ibrahim Tanko Muhammad, su amince da dage karar zuwa ranar 2 ga Maris, 2020.

Da duminsa daga kotun koli: An dage zaman sake duba shariar Imo zuwa watan gobe
Da duminsa daga kotun koli
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel