Lauyan Maryam Booth ya shigar da karar Deezell a babban kotun Kaduna

Lauyan Maryam Booth ya shigar da karar Deezell a babban kotun Kaduna

Wani fitaccen ‘Dan gwagwarmaya Mai kare hakkin Jama’a, Muhammad Lawal Gusau, ya shigar da kara a gaban babban kotun tarayya da sunan Maryam Booth.

Muhammad Lawal Gusau ya kai karar Ibrahim Rufai wanda aka fi sani da Deezell kotu ne bisa zarginsa da ake yi da laifin yada bidiyon tsiraicin wannan Budurwa.

Lawal Gusau ya shigar da kara ne a kotun tarayya da ke zama a Garin Kaduna. Lauyan ya na zargin Mawakin da keta alfarmar ‘Yar wasan da ya ke karewa.

Taururuwar Kannywood ta zargi Ibrahim Rufai da laifin daukar ta bidiyonta a cikin wani irin hali da bai kamata ba, wanda kuma ya wallafa bidiyon a kan yanar gizo.

Lauyan Maryam Booth ya bukaci kotu ta sa Ibrahim Rufai ya biya Naira miliyan 10 a sakamakon ta’adin da ya yi, tare da fitowa ya bada hakuri a gidajen jaridu uku.

KU KARANTA: An yi wa karamar yarinya ciki har ta mutu a Jihar Sokoto

Lauyan Maryam Booth ya shigar da karar Deezell a babban kotun Kaduna
Fitacciyar 'Yar wasar fim Maryam Booth ta kai Deezell kotu
Asali: Twitter

Booth ta fadawa Alkali ta bakin Lauyanta cewa wannan tonon silili da aka yi mata ya jawo mata cin mutunci kamar yadda Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto jiya.

A takardar karar da aka gani a Ranar Litinin, 17 ga Watan Fubrairu, ana tuhumar Deezell da keta alfaramar ‘Yar wasan kwaikwayon, wanda hakan ya sabawa doka.

Wallafa bidiyon shararriyar Tauraruwar tsirara ya sabawa sashe na 34, 35, 37, 38 da kuma 46 na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda aka yi wa garambawul a 1999.

A na sa bangaren, Mista Ibrahim Rufai ya karyata wannan zargi, ya kuma bukaci Booth ta janye wannan magana, a karshe har ya kai kararta da wasu gaban kotu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel