Majalisar wakilai ta bayar da kwangilar sayen motocin alfarma guda 400
Majalisar wakilai ta yi odan motocin alfarma guda 400 kirar Toyota Camry 2020 domin amfanin yan majalisar su 360, kamar yadda shuwagabannin majalisar suka yanke hukunci a wani taro da suka yi a ranar 5 ga watan Feburairu.
Jaridar Punch ta ruwaito wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da amincewar majalisar na sayo motocin alarma guda 400, sai bata bayyana farashin da majalisar za ta sayo motocin a kai ba.
KU KARANTA: Harin yan bindiga: Buhari ya tura manyan jami’an gwamnati zuwa jahar Katsina
Majiyar Legit.ng ta tuntubi wakilin kamfanin motocin Elizade Nigeria Limited wanda yace har yanzu babu irin wannan motar a Najeriya, domin kuwa bata riga ta shigo ba, amma yace Toyoto Camry 2019 ta kai naira miliyan 26.75, yayin da V6 dinta ta kai N35.75m.
Sai dai wani bincike da majiyarmu ta yi a shafin yanar gizo na Toyota ya nuna motar Toyota Camry 2020 ta kai naira miliyan 9 zuwa naira miliyan 12.6, banda kudin daukota daga Japan zuwa Najeriya, wanda ya kai kashi 70 na kudin motar, da kuma sauran harajin da za’a biya musu wajen shigowa.
A yayin zaman na yan majalisar, sun nuna rashin gamsuwarsu da amfani da motocin gida, inda suka fifita motocin kasashen waje, wanda aka harhadasu a kasar waje ba wanda aka harhadasu a Najeriya ba.
Majiyar daga majalisa ta bayyana cewa: “Toyota Camry 2020 ake bukata, Manga zai kawo guda 300, yayin da mutumin daya sayo ma majalisar dattawa kuma zai kawo sauran gudan 100.” Inji shi.
Zuwa yanzu dai an raba manyan motocin alfarma kirar Toyota Land Cruiser guda 14 ga shuwagabannin majalisar da shuwagabannin wasu zababbun kwamitoci.
A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura tawagar gwamnatin tarayya zuwa jahar Katsina domin ta jajanta ma gwamnan jahar Katsina, Sarkin Katsina da ma kafatanin al’ummar jahar Katsina bisa hare haren yan bindigan da suke fama da shi.
Tawagar ta isa Katsina ne a ranar Litinin, 17 ga watan Feburairu a karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Abba Kyari, wanda Buhari ya umarcesu su samu masa cikakken bayani game da matsayin tsaro a jahar.
Cikin sakon taya alhini da Abba Kyari ya isar a Katsina, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa bisa mutuwar mutane 31 a harin da yan bindiga suka kai karamar hukumar Batsari, sa’annan ya jajanta ma iyalan mamatan.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng