Sokoto: Ana zargin Darekta, wasu Mutum 2 da yi wa wata Yarinya ciki

Sokoto: Ana zargin Darekta, wasu Mutum 2 da yi wa wata Yarinya ciki

Darektan sha’anin kudi a gwamnatin Sokoto, da Ahmad Yahya Nawawi, da wani Ma’aikacin jihar sun fada hannun hukuma da laifin yi wa wata ‘Yar shekara 14 ciki.

Ana zargin wadannan Bayin Allah uku da ke aiki a hukumar kula da kasa da rabon filaye na jihar Sokoto da yin lalata da karamar yarinyar da ke tallar ruwa a kan hanya.

Tuni dai har an maka su a babban ofishin hukumar NAPTIP inda su ka amsa laifinsu da kansu. Sai dai kuma daga baya, wadannan mutane sun fito sun karyata zargin.

Ahmad Yahya Nawawi ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewa sharri ake yi masa domin a bata masa suna. Yahya Nawawi ya bayyana cewa siyasa ta shiga cikin lamarin.

Amma kuma wata Goggon wannan Yarinyar, ta bayyana cewa kudi aka ba Mahaifin wannan yarinya domin ya yi gum. A cewarta, an ba shi N250, 000 har ya saye fili.

KU KARANTA: Dattawa ba su yadda da yadda kuri'ar zaben Matar da aka yi a Bauchi ba

Sokoto: Ana zargin Darekta, wasu Mutum 2 da yi wa wata Yarinya ciki
Hukumar NAPTIP ta na farautar masu cin zarafin kanana yara
Asali: Facebook

Malam Muhammadu wanda shi ne Mahaifin wannan Baiwar Allah, ya musanya zargin, ya bayyana cewa wadanda ake zargi sun ba shi N50, 000 ne a lokacin da ya yi jinya.

A game da batun janye kara a kotu kuwa, ya bayyana cewa ya yi hakan ne a matsayinsa na Musulmi wanda ya rungumi kaddara, ba wai don an ba shi wasu makudan kudi ba.

Har ila yau, Malam Muhammadu ya bayyana cewa wadannan mutane da ake zargi da yi wa ‘Diyarsa fyade, sun yi alkawarin daukar dawainiyar karatunta da zarar ta haihu.

Goggon Yarinyar, Maryam Yusuf, ta bayyana cewa jim kadan bayan yarinyar ta haihu ta rasu, a sakamakon asarar jini da ta yi. Ta ce dama Mahaifiyar yarinyar ta rabu da Uban.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel