Dan bautan kasa ya haukace bayan ya zane dalibin da yake koyarwa a Akwa Ibom

Dan bautan kasa ya haukace bayan ya zane dalibin da yake koyarwa a Akwa Ibom

Wani matashi mai yi ma kasa hidima a karkashin tsarin NYSC, mai suna Corper Saeed Olakunle ya samu tabuwar hankali bayan ya zane wani dalibi a makarantar da yake koyarwa a garin Nsit Ibom na jahar Akwa Ibom.

Opera News ta ruwaito Corper Saeed Olakunle ya ladabtar da dalibin ne saboda rashin mayar da hankali a yayin da yake koyawar dasu darasin lissafi, kamar yadda abokansa da suke zama a gida daya suka tabbatar.

KU KARANTA: Za mu maka Buhari gaban kotu a kan wa’adin manyan hafsoshin tsaro – Falana

Dan bautan kasa ya haukace bayan ya zane dalibin da yake koyarwa a Akwa Ibom
Saeed
Asali: Twitter

Makwabtan Corper Saeed Olakunle sun bayyana cewa bayan tashinsa daga baccin rana ne sai suka lura yana wasu dabi’un da bai sab aba, yana fitsari a cikin dakinsa kuma furta wasu kalamai da marasa ma’ana.

Nan da nan abokin zamansa ya kira sauran makwabtansu domin neman dauki, amma koda suka yi kokarin tsare shi a wuri guda, sai kawai ya balle ya ranta ana kare, da kyar suka kamo shi.

Sai dai abokan Corper Saeed Olakunle suna ganin cewa wannan hauka da ya samu baya rasa nasaba da kulumboto da wannan dalibi da ya buga ya yi masa, kuma karin tashin hankali shi ne yaron bai kara zuwa makaranta ba.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura tawagar gwamnatin tarayya zuwa jahar Katsina domin ta jajanta ma gwamnan jahar Katsina, Sarkin Katsina da ma kafatanin al’ummar jahar Katsina bisa hare haren yan bindigan da suke fama da shi.

Tawagar ta isa Katsina ne a ranar Litinin, 17 ga watan Feburairu a karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Abba Kyari, wanda Buhari ya umarcesu su samu masa cikakken bayani game da matsayin tsaro a jahar.

Cikin sakon taya alhini da Abba Kyari ya isar a Katsina, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa bisa mutuwar mutane 31 a harin da yan bindiga suka kai karamar hukumar Batsari, sa’annan ya jajanta ma iyalan mamatan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel