Matawalle ya dauki mataki kan hukuncin kisa da Saudiyya ta yanke wa Malamin Najeriya

Matawalle ya dauki mataki kan hukuncin kisa da Saudiyya ta yanke wa Malamin Najeriya

Ibrahim Ibrahim dai dan Najeriya ne daga jihar Zamfara wanda a kwanakin baya jiharsa tayi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ceto rayuwarsa. Malamin dai ya dau shekaru uku a garkame a kasar Saudi Arabia bayan da aka zargesa da safarar miyagun kwayoyi. Yayi kira ga gwamnatin jiharsa da ta cece shi don bai aikata laifin da ake zarginsa da shi ba.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta bayyana, gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Bello Matawalle ya tura wakilai zuwa kasar Saudi Arabia don ceto rayuwar dan asalin jihar Zamfaran da ke fuskantar hukuncin kisa a kasar.

Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa wakilan gwamnatin sun hada da kungiyar lauyoyi a cikinsu.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da Zailani Bappa, mai bada shawara na musamman ga gwamnan a kan yada labarai, ya mika ga manema Labarai a garin Gusau a ranar Litinin.

Dan asalin jihar Zamfara din mai suna Ibrahim Ibrahim na fuskantar hukuncin kisa ne sakamakon shiga kasar Saudi Arabia da miyagun kwayoyi da yayi.

Matawalle ya dauki mataki kan hukuncin kisa da Saudiyya ta yanke wa Malamin Najeriya
Matawalle ya dauki mataki kan hukuncin kisa da Saudiyya ta yanke wa Malamin Najeriya
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Diyar gwamnan Bauchi ta yi wa masu fakewa da hukuncin Maryam Sanda suna yi wa musulunci batanci raddi

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, kotu biyu ne suka wanke malamin daga zargin da ake masa tare da bayyana cewa ba shi ne mai mallakin miyagun kwayoyin ba. Hakan ne kuwa yasa hukumomin kasar Saudi Arabia din suka daukaka kara zuwa kotun gaba wacce ake tsammanin za ta yanke hukuncin a yau Talata 18 ga watan Fabrairu 2020.

Amma kuma gwamnan ya samu shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da bukatar gwamnatin tarayya ta sa hannu wajen kokarin wanke Ibrahim tare da tseratar da ransa.

Tuni dai shugaban kasa ya umarci ministan shari'a Abubakar Malami, da ya shiga maganar.

Wakilan gwamnatin da suka hada da lauyoyi sun samu jagorancin kwamishinan aiyuka na musamman da kuma mai bada shawara ta musamman a kan harkokin shari'a na jihar.

Ana bukatar wakilan su zama a kotun tare da kiyaye shari'ar da za a yi a Makkah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel