Arewa na halaka kanta da kanta - Sarki Sanusi II

Arewa na halaka kanta da kanta - Sarki Sanusi II

Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce Arewa za ta ci gaba da tarwatsa kanta matukar ba ta sauya daga yadda take ba. Sarkin yayi wannan maganar ne a ranar Litinin a gidan gwamnatin jihar Kaduna yayin bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Nasir El-Rufai karo na 60.

Sanusi ya ce a matsayin shugaba, maimaita abinda ka tarar ana yi tare da tsammanin za ka banbanta ba dai-dai bane.

Ya kara da cewa, canji zai samu ne a Arewa idan aka fara yin abubuwa mabanbanta.

Ya jinjinawa salon gyaran bangaren ilimi na gwamna El- rufai. Ya ce hakan ne kawai zai iya tseratar da Arewa.

"Dai-dai ne idan gwamna ya bi salon da ya tarar na mulki a cewar mutanen Arewa. Amma ba dai-dai bane gaskiya idan ya bi salon da bai kawo wani canji ga yankin. Idan kuwa shugaba ko mai mulki yayi hakan, zamu iya cewa yana daga cikin matsalar yankin nan," Sanusi ya ce.

"Babban canji a Arewa zai zo ne bayan mun gano cewa sai mun banbanta da sauran. Idan arewa bata canza ba, za ta halaka kuwa. Idan bamu canza ba, akwai lokacin da mun sani da zai zo." in ji shi.

"Sauran yankuna a kasar nan na zuba kudi wajen ilimantar da yaransu tare da yaye dalibai daga manyan makarantu amma mu bamu yin haka. Wadannan yankunan ba zasu zuba ido su kasa hayewa shugabancinmu ba saboda ba daga yankin da ya kamata suke ba, bayan mun gaza gina 'ya'yanmu." cewar basaraken

Sarkin ya bayyana cewa, babu wani shugaba a Arewa da zai samu farin ciki bayan yana zagaye da matsaloli a yankin.

Arewa na halaka kanta da kanta ne - Sarki Muhammadu Sanusi
Arewa na halaka kanta da kanta ne - Sarki Muhammadu Sanusi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An yi zabe a Bauchi don raba gardama tsakanin samari 2 da ke neman auren wata budurwa (Hotuna)

"Babu wani shugaba a Arewa da zai ce yau yana cikin farin ciki," Sanusi ya ce.

"Ba zaka zama cikin farin ciki a Arewa ba bayan kashi 87 na talaucin Najeriya na Arewa. Ba yadda za a yi kayi farin ciki bayan yara da yawa basu zuwa makaranta a yankin nan. Ba yadda za a yi kayi farin ciki bayan akwai matsalar Boko Haram." Basaraken ya kara da cewa.

Kamar yadda jaridar the Cable ta ruwaito, ya kara da cewa "Muna taya Nasir murnar zagayowar ranar haihuwarsa kuma ba ma so yayi farin ciki a matsayin shugaba. Saboda farin ciki na zuwa ne bayan da jiha ta kai wani mataki na daukaka tare da mutanenta."

Ya ce ya kamata a taya El-rufai murna ne a matsayin jami'in gwamnati da ke kokarin shawo kan manyan matsalolin yankin shi.

"Idan aka duba yadda gwamnan jihar Kaduna yayi da kasafin kudin shi ta yadda kashi 40 ya ke a bangaren ilimi, zamu iya cewa wannan ce hanyar da za ta tseratar da arewa," ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel