Kisan mutane 30 a Auno: FG ta aika da kayan tallafi

Kisan mutane 30 a Auno: FG ta aika da kayan tallafi

A ranar Litinin ne gwamnatin tarayya ta aikawa da mazauna Auno kayan tallafi. Auno dai kauye ne da yake da makwabtaka da Maiduguri a jihar Borno, wanda cikin kwanakin nan mayakan Boko Haram suka kai hari inda suka halaka mutane 30.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci Maiduguri, babban birnin jihar Borno don jajantawa a kan lamarin da ya faru a makon da ya gabata.

An yi wa Buhari ihun 'bama so, bama yi' a jihar. Fusatattun mazauna yankin ne kuwa suka yi hakan sakamakon kisan gillar da aka dade ana yi musu.

Amma fadar shugaban kasa ta ce abokan adawa ne suka dau nauyin wannan ihun. Fadar ta kara da cewa wannan ihun ba yana nufin ba a son gwamnatin manjo janar din mai ritaya bane.

Kisan mutane 30 a Auno: FG ta aika da kayan tallafi
Kisan mutane 30 a Auno: FG ta aika da kayan tallafi
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Diyar gwamnan Bauchi ta yi wa masu fakewa da hukuncin Maryam Sanda suna yi wa musulunci batanci raddi

A ranar Litinin, ma'aikatar jin kai da tallafi ga 'yan kasa tare da hukumar kula da ci gaban yankin ne suka mika kayan abinci da wadanda ba na abinci ba ga kauyen Auno.

Babban daraktan hukumar kula da habaka yankin Arewa maso gabas, Mohammed Alkali , yayin jawabi ga jama'ar kauyen, ya ce "A madadin gwamnatin tarayya, hukumar nan ta kawo kayan abinci da kayan sassauci na gaggawa gareku don nuna jin kai da tausayin abinda ya faru da ku."

Kamar yadda ya sanar, kayan tallafin da jinkan sun hada da barguna 5000, buhunan wake 1,000, katifu 1,000 , kwaleyen man girki 200, buhunan shinkafa 1,000, kwalayen tumatir 50, kwalayen magin girki 50 da kuma tabarmi 1,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel