Yanzu Yanzu: Babu wanda ya kai mani hari a jahar Kaduna – Ministan sufuri

Yanzu Yanzu: Babu wanda ya kai mani hari a jahar Kaduna – Ministan sufuri

- Ministan sufuri, Mista Rotimi Amaechi ya karyata rade-radin cewa ya tsallake rijiya da baya a hannun yan bindiga a jahar Kaduna

- Amaechi ya mayar da martani ne ga Aisha Yesufu wacce ta ce ministan ya ci na kare a lokacin da maharan suka far masu

- Mun dai ji cewa wasu mahara sun kai farmaki a kan hanyar tashar jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja

Ministan sufuri, Mista Rotimi Amaechi ya karyata rade-radin cewa ya tsallake rijiya da baya a yayin da wasu mahara suka kai farmaki a kan hanyar tashar jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja.

A cewar Amaechi babu yan bindiga ko masu garkuwa da mutane da suka kai masa hari.

Amaechi ya maida wa jagorar fafutukar neman dawo da yan matan Chibok Aisha Yesufu martani, inda yace zagi ko cin mutunci ba zai sauya gaskiyar cewa babu wanda ya kai masa hari a Kaduna a daren jiya Lahadi.

Yanzu Yanzu: Babu wanda ya kai mani hari a jahar Kaduna – Ministan sufuri
Yanzu Yanzu: Babu wanda ya kai mani hari a jahar Kaduna – Ministan sufuri
Asali: UGC

Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: “Baiwar Allah ba a kai mani hari ba, ban ga kowasu mahara, yan bindiga ko masu garkuwa da mutane ba kuma ban tsallake rijiya da baya ba, ban tsere ba..” zagi ko cin mutunci ba zai sauya gaskiyar cewa ba a kai mani hari ba, a Kaduna a daren jiya.”

A baya mun ji cewa Fasinjojin jirgin kasa da dama sun tsallake rijiya da baya yayin da wasu gungun miyagu yan bindiga suka kaddamar da farmaki a kan hanyar dake gab da tashar jirgin kasa dake tashi daga Kaduna zuwa Abuja, a unguwar Rigasa.

Daily Nigerian ta ruwaito lamarin ya faru ne da daren Lahadi, 16 ga watan Feburairu, kim kadan bayan jirgin ya sauke fasinjojinsa, inda yawancinsu suka kama sabuwar hanyar da ta tashi daga Rigasa zuwa Mando, daga cikinsu har da ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

KU KARANTA KUMA: Hauwa Yunus: Labarin yar shekara 24 da ke garkuwa da mutane wacce ke yaudarar maza da kyawunta

Majiyar Legit.ng ta kara da cewa yan bindigan sun yi shirin kwantan bauna ne a kan titin na Mando sa nufin kai ma duk wanda ya bi hanyar farmaki, hangen ayarin motoci da suka yi da wuya sai suka bude wuta, nan da nan Sojoji da Yansanda suka mayar musu da biki aka yi ta musayar wuta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel