Amarya ta tsira yayin da hadarin mota ya halaka kawayen amarya 22 a Katsina

Amarya ta tsira yayin da hadarin mota ya halaka kawayen amarya 22 a Katsina

Wani mummunan hadari ya lakume akalla mutane 22, yayin da wasu 11 suka samu munanan rauni, a kan titin Kankia-Danja a cikin karamar hukumar Kafur, yayin da mutane uku kacal suka sha daga hadarin.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hadarin ya faru ne tsakanin wasu motocin J5 guda biyu dake dauke da mutane 36, kamar yadda mai magana da yawun hukumar kare haddura ta kasa, FRSC, reshen jahar Katsina, Abubakar Usman ya bayyana.

KU KARANTA: Harin yan bindiga: Ministan sufuri Amaechi ya tsallake rijiya da baya a jahar Kaduna

Abububar ya bayyana ma gidan talabijin na Channels cewa mutane 11 sun samu munana rauni baya ga 22 da suka mutu, amma yace akwai wasu guda uku da suka tsallake rijiya da baya a hadarin daya kona motocin biyu duka.

Wani shaidan gani da ido, Shafiu Suleiman yace wadanda hadarin ya rutsa dasu akwai Amarya, kawayenta, wasu mata da kananan yaransu dake cikin yan rakiyar amaryar zuwa gidan mijinta.

Sai dai wani da lamarin ya faru a gabansa yace amaryar da wani direba na daga cikin wadanda suka sha daga hadarin, sai dai hukumar kare haddura bata tabbatar da wannan bayani ba sakamakon har zuwa lokacin hada wannan rahoto basu kammala tantance mutanen da hadarin ya shafa ba.

Kaakakin FRSC, Abubakar Usman yace sun garzaya da wadanda hadarin ya shafa zuwa babban asibitin garin Malumfashi domin kulawa da wadanda suka jikkata, yayin da su kuma wadanda suka mutu za’a baiwa iyalansu takardun tabbatar da rasuwarsu.

Amma yace wadanda wuta ta konasu ta yadda ba’a iya ganesu tuni aka yi musu jana’iza, aka binnesu kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

A wani labarin kuma, rundunar Sojan sama ta Najeriya ta bayyana rahoton dake yawo a kafafen sadarwa na cewa wai dakarunta sun kashe mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram guda 250, a matsayin labarun kanzon kurege.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan labari ya fara yawo a kafafen sadarwa ne tun a ranar 13 ga watan Feburairu, kuma wai ya fito ne daga wajen wani mutumi mai suna ‘Comr Aminu Shuaibu Musawa, kamar yadda hukumar sojan sama ta bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel