Janar Babangida ya yi magana game da rashin tsaro, gidan soji, da aure

Janar Babangida ya yi magana game da rashin tsaro, gidan soji, da aure

Ku na da labari cewa tsohon shugaban Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, wanda ya yi mulki a lokacin Soja, ya yi wata hira ta musamman da Jaridar Daily Trust a karshen makon nan.

Mun tsakuro manyan batutuwan da tsohon Sojan ya tattauna a su a wannan hira ta su:

1. Yakin Boko Haram

Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, ya bayyana cewa dole Sojojin Najeriya su maida hankali wajen samun bayanan sirri game da ‘Yan ta’addan kafin a iya kai ga nasara a yakin.

2. Shiga gidan Soja

Janar Yakubu Gowon da wasu manyan Sojojin Arewa su na cikin wadanda su ka tunzura Ibrahim Babangida ya shiga aikin Soja a lokacin Firayim Minista Abubakar Tafawa-Balewa ya na mulki.

3. Karatun Al-Kur’ani

IBB kamar yadda ake yi masa lakabi, mutum ne mai yawan karatun Al-Kur’ani. Sai dai Jama’a da-dama ba su san wannan ba. Babangida ya ce Duniya ta kan masa dadi idan ya na karatu.

KU KARANTA: Yadda za a yi maganin rikicin Boko Haram a Najeriya - IBB

Janar Babangida ya yi magana game da rashin tsaro, gidan soji, da aure
Janar Ibrahim Babangida a gidansa tare da wasu 'Yan siyasan Najeriya
Asali: Depositphotos

4. Rashin aure

A game da yadda ya ke rayuwa ba tare da Matar aure ba, tsohon shugaban kasar ya nuna cewa ‘Ya ‘yansa su na taimaka masa. Sojan yakin ya kuma bayyana cewa bai da niyyar sake aure a yanzu.

5. Kifar da Gwamnati

Tsohon shugaban na Najeriya ya yi magana game da juyin mulki a Najeriya inda ya ce hambarar da gwamnati ya samo asali ne tun 1952 har zuwa shekarun 1990 a kasashen Afrika da-dama.

6. Rashin tsaro

Ibrahim Babangida ya yi magana game da Dajin Sambisa da Boko Haram su ka karbe. A na sa ra’ayin kuma, aiki ne ya yi wa ‘Yan Sanda da Soji yawa har ake kokarin kawo Dakarun Amotekun.

Ibrahim Badamasi Babangida ya rike mukamai a Najeriya wanda su ka hada Shugaban hafsun soji, har ya samu damar zama shugaban kasa bayan ya kifar da gwamnati a shekarar 1985.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel