Hukuncin kotun koli: Allah ya warkar da jahar Bayelsa – In ji Diri

Hukuncin kotun koli: Allah ya warkar da jahar Bayelsa – In ji Diri

- Sanata Douye Diri, zababben gwamnan Bayelsa ya bayyana cewa Allah ya warkar da jahar ta hukuncin kotun koli wacce ta soke zaben dan takarar jam’iyyar APC, David Lyon sannan ta dawo dashi a matsayin wanda ya lashe zaben

- Diri ya yi magane ne yayinda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ke gabatar masa da takardar shaidar cin zabe a hedkwatar hukumar da ke Abuja

- Hukumar zabe ta Diri da mataimakinsa, Lawrence Ewhrujiakpo da takardarsu na shaidar cin zabe

Zababben gwamnan jahar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya bayyana cewa Allah ya warkar da jahar Bayelsa ta hukuncin kotun koli wacce ta soke zaben dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) David Lyon sannan ta dawo dashi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Diri ya yi magane ne yayinda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ke gabatar masa da takardar shaidar cin zabe a hedkwatar hukumar da ke Abuja.

Hukuncin kotun koli: Allah ya warkar da jahar Bayelsa – In ji Diri
Hukuncin kotun koli: Allah ya warkar da jahar Bayelsa – In ji Diri
Asali: Facebook

A cewarsa: “Ba zan taba mantawa da bangaren shari’a ba, shine madogarar talaka na karshe. Da wannan abun da ya faru, Allah ya warkar da jaharmu ta Bayelsa. A tsakakkanin wannan lokacin, Allah ya kai mu ga tafarkin sasanci da yafiya."

An gabatar wa da Diri da mataimakinsa, Lawrence Ewhrujiakpo da takardarsu na shaidar cin zabe, a wani taro da aka gabatar a hedkwatar INEC.

KU KARANTA KUMA: Hukuncin kotun koli kan Bayelsa hatsari ne ga damokradiyyar Najeriya - APC

A baya mun ji cewa zanga-zanga ya barke a sassan Yenegoa, babbar birnin jihar Bayelsa kan shari'ar kotun kolin tarayya da ta hana rantsar da Cif David Lyon, a matsayin gwamnan jihar.

Dubunnan mata sun tare manyan hanyoyin jihar domin inda suka lashi takobin cewa babu wanda za'a rantsar gwamnan jihar Bayelsa yau.

Ana saura awanni kasa da 24 da rantsar da sabon gwamna, kotun koli a ranar Alhamis ta fitittiki David Lyon a matsayin zababben gwamnan jihar Bayelsa tare da mataimakinsa, Biobarakuma Degi-Eremienyo bayan sun lashe zaben 16 ga Nuwamba 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng