Muddin ina a matsayin Shugaban kasa, ba za a taba auren jinsi ba a Rasha - Putin

Muddin ina a matsayin Shugaban kasa, ba za a taba auren jinsi ba a Rasha - Putin

- Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya ce ba zai taba halasta auren jinsi ba a Rasha muddin yana a matsayin Shugaban kasar

- Shugaban kasar mai shekara 67 ya yi adawa da rushe wannan al’ada mai karfi ta uwa da uba ba

- A watan da ya gabata, Dmitry Medvedev, Firaye ministar Rasha da gwamnatin Rasha baki daya suka ajiye aiki bayan shugaba Vladimir Putin ya nemi gyara a kundin tsarin mulki wacce za ta bari ya ci gaba da kasancewa a mulki har illa-ma-shaa-Allah

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya ce ba zai taba halasta auren jinsi ba a Rasha muddin yana a matsayin Shugaban kasar.

Da ya ke magana a ranar Alhamis, 13 ga watan Fabrairu a Kremlin, inda ya hadu da wata hukumar kasar don tattauna sauye-sauye a kundin tsarin mulkin Rasha, Shugaban kasar mai shekara 67 ya yi adawa da rushe wannan al’ada mai karfi ta uwa da uba zuwa ga abunda ya kira a matsayin “iyaye na” 1 da “iyaye na 2”.

“Idan dai a kan ‘iyaye na 1 ’da ‘iyaye na 2’ ne, na rigada na yi magana gameda lamarin a bainar jama’a kuma zan kara maimaitawa: muddin ina a matsayin Shugaban kasa hakan ba zai taba faruwa ba. Za a kasance ne da uwa da uba,” in ji Putin.

A watan da ya gabata, Dmitry Medvedev, Firaye ministar Rasha da gwamnatin Rasha baki daya suka ajiye aiki bayan shugaba Vladimir Putin ya nemi gyara a kundin tsarin mulki wacce za ta bari ya ci gaba da kasancewa a mulki har illa-ma-shaa-Allah.

Yayinda ya ke jawabi ga majalisarsa a wannan lokaci, Putin ya nemi ayi kuri’ar raba gardama kan gyara kundin tsarin mulkin Rasha don kara karfin majalisa yayinda ake ci gaba da tsarin shugabanci mai karfi.

KU KARANTA KUMA: Hukuncin kotun koli kan Bayelsa hatsari ne ga damokradiyyar Najeriya - APC

“Ina ganin akwai bukatar al’umman kasar su gudanar da kuri’a kan bukatar gyara kundin tsarin mulkin kasar,” in ji Putin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel