Lauyoyi sun bukaci a kama Oshiomhole
- Revolutionary Lawyers’ Forum, ta nemi jami'an tsaro da su kama shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole
- Kungiyar ta kuma nemi da a tuhume shi a kan laifin cin amanar kasar
- Kiran ya biyo bayan kalaman da Oshiomhole ya yi cewa ba za a rantsar da kowa kan kujerar gwamnan jahar Bayelsa ba, jim kadan bayan kotun koli ta tsige zababben gwamnan jahar wanda ya kasance dan takarar jam'iyyar APC
Wata kungiyar lauyoyi mai suna Revolutionary Lawyers’ Forum, ta nemi jami'an tsaro da su kama shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole, sannan su tuhume shi a kan laifin cin amanar kasar.
Jaridar TheCable ta ruwaito cewa shugaban kungiyar Tope Akinyode ya ce sun yi kiran ne saboda kalaman da Oshiomhole ya yi cewa ba za a rantsar da kowa kan kujerar gwamnan jahar Bayelsa ba, jim kadan bayan kotun koli ta tsige zababben gwamnan jahar wanda ya kasance dan takarar jam'iyyar APC.
Alkalan kotun sun bukaci a rantsar da dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP, wanda shi ne ya zo na biyu a zaben.
Mista Tope ya ce kalaman da Oshiomhole ya yi tamkar wani yunkuri ne na kifar da gwamnatin jihar ta Bayelsa.
Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce: “Muna kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta kamawa da kuma hukunta Oshiomhole a kotu bisa aikata laifin cin amanar kasa."
A baya mun ji cewa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta soki hukuncin kotun koli wacce ta tsige dan takararta, David Lyon, a matsayin zababben gwamnan jahar Bayelsa.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa jam’iyyar na iya shigar da bukatar sake duba ga hukuncin kotun koli wacce ta tsige dan takararta, David Lyon, a matsayin gwamnan jahar Bayelsa.
KU KARANTA KUMA: Gwamnan Bauchi ya taya Douye Diri murna kan hukucin kotun koli a zaben gwamnan Bayelsa
Da ya ke martani kan hukuncin kotun kolin, Oshiomhole ya ce tuni jam’iyyar ta tuntubi lauyoyinta kan matakin da ta ke shirin dauka don tabbatar da ganin an dawo wa da Lyon hakkinsa.
Babbar kotun ta tsige Mista Lyon a ranar Alhamis, 13 ya watan Fabrairu kan hujjar cewa mataimakinsa, Biobarakuma Degi-Eremienyo, ya gabatar da satifiket na bogi ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a yayin zaben.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng