Gwamnan Bauchi ya taya Douye Diri murna kan hukucin kotun koli a zaben gwamnan Bayelsa

Gwamnan Bauchi ya taya Douye Diri murna kan hukucin kotun koli a zaben gwamnan Bayelsa

- Gwamnan jahar Bauchi ya yi martani ga nasarar takwararsa na jahar Bayelsa a kotun koli

- Gwamna Bala Mohammed a wani jawabi ya bayyana nasarar da jam’iyyarsa ta yi a kotun koli a matsayin babban rabo ga jahar Bayelsa

- A ranar Alhamis, 13 ga watan Fabrairu ne kotun kolin ta soke zaben David Lyon da mataimakinsa, Biobarakuma Degi-Eremieoyo na APC

Gwamnan jahar Bauchi, Bala Mohammed ya taya dan takarar PDP Sanata Douye Diri da mataimakinsa, Lawrence Ewhrudjakpo murna kan nasararsu a kotun koli a ranar Alhamis, 13 ga watan Fabrairu.

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa an bayyana sakon Mohammed ne a wani jawabi ta hannun Lawal Muazu Bauchi, hadimin gwamnan na musamman kan shafukan zamani. Gwamnan Bauchin a sakonsa ya bayyana nasarar Diri a matsayin babban rabo ga jahar Bayelsa.

Gwamnan Bauchi ya taya Douye Diri murna kan hukucin kotun koli a zaben gwamnan Bayelsa
Gwamnan Bauchi ya taya Douye Diri murna kan hukucin kotun koli a zaben gwamnan Bayelsa
Asali: UGC

Mohammed wanda ya yi aiki a matsayin Shugaban kungiyar kamfen din zaben gwamna na 2019 a jahar Bayelsa, ya yi godiya ga ahlin PDP da suka bashi damar hawa wannan matsayin.

KU KARANTA KUMA: Ziyarar Borno: Ku ba Buhari hakuri yanzun nan – Kungiya ga gwamnan APC da hadimansa

A bangare guda mun ji cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta soki hukuncin kotun koli wacce ta tsige dan takararta, David Lyon, a matsayin zababben gwamnan jahar Bayelsa.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa jam’iyyar na iya shigar da bukatar sake duba ga hukuncin kotun koli wacce ta tsige dan takararta, David Lyon, a matsayin gwamnan jahar Bayelsa.

Da ya ke martani kan hukuncin kotun kolin, Kwamrad Oshiomhole ya ce tuni jam’iyyarsa ta tuntubi lauyoyinta kan matakin da ta ke shirin dauka a nan gaba don tabbatar da ganin an dawo wa da Lyon hakkinsa.

Babbar kotun ta tsige Mista Lyon a ranar Alhamis, 13 ya watan Fabrairu kan hujjar cewa mataimakinsa, Biobarakuma Degi-Eremienyo, ya gabatar da satifiket na bogi ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a yayin zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel