Abinda Zulum ya faɗa a kan ziyarar da Buhari ya kai Borno

Abinda Zulum ya faɗa a kan ziyarar da Buhari ya kai Borno

- Duk da koma baya da tabarbarewa da ake samu a tsaron cikin gida Najeriya, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya ce Buhari na mayar da hankali

- Gwamnan jihar Borno, ya mika sakon ban gajiya da kuma godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan ta'aziyyar da ya kai jihar

- Gwamnan ya bayyana cewa, jin kan da shugaban kasar ke nunawa jihar Borno babu ko shakka alamu ne na son kawo karshen Boko Haram

Duk da koma baya da ake samu da tabarbarewa a fannin tsaro a jihar Borno, babu wanda zai ce shugaban kasa Muhammadu Buhari baya mayar da hankali a kan tsaro, in ji Gwamna Babagana Zulum.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, gwamnan ya saki sakon ne a daren jiya Alhamis ta hannun mai magana da yawunsa, Malam Isa Gusau. Gwamnan ya mika godiyarsa ta yadda shugaban kasar ya nuna kulawarsa da damuwa har ya ziyarci Maiduguri a ranar Laraba.

Abinda Zulum ya faɗa a kan ziyarar da Buhari ya kai Borno
Abinda Zulum ya faɗa a kan ziyarar da Buhari ya kai Borno
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bayan martanin da Diri na PDP yayi, ya kama hanyar Yenagoa don rantsarwa

“Yadda ka nuna tausayinka ga jama’ar jihar Borno abin godiya ne kuma babu shakka a kudirinka. A takaice dai karara yake hakan. Ziyarar da ka kawo Maidugurin bayan dawowarka kasar nan na nuna yadda kake kaunar jama’ar Borno.” Gwamnan ya ce.

“Ziyarar da ka kawo tafi karfin jin kai. Ta karfafa mu ballantana yadda kake sauraronmu a kodayaushe tare da tabbatar mana da cewa a shirye kake ka kawo karshen Boko Haram. Sanannen abu ne tun daga ranar farko da ka hau kujerarka, ka saka matsalar tsaronmu gabanka.” Zulum ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel