Tun kafin a rantsar da ni a aka bani gwarzon gwamnonin 2019 - David Lyon

Tun kafin a rantsar da ni a aka bani gwarzon gwamnonin 2019 - David Lyon

Zababben gwamnan jihar Bayelsa, David Lyon wanda kotun koli ta tube a yau Alhamis ya bayyana cewa tun kafin a rantsar da shi ne aka bashi gwarzon gwamnoni na shekarar 2019. Gwamnan ya bayyana cewa an bashi wannan karramawar ne tun kafin a rantsar da shi.

Tubabben gwamnan ya wallafa wannan bidiyon ne a shafinsa na tuwita. Duk da dai har a halin yanzu ba a san daga inda kyautar karamcin ta fito ba, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Amma a yayin kwatanta karramawar, ya ce “abin na Ubangiji ne”. Lyon ya kara da cewa bai saba karbar ire-iren wadannan kyautukan ba amma ya karba na wannan karon ne saboda ku.

“Tun kafin in hau karagar mulki, ba a rantsar dani ba a matsayin gwamnan aka bani gwarzon gwamnoni na 2019. Kuma hakan zan iya cewa abin na Allah ne,” ya ce.

A yau Alhamis ne kotun koli ta kwace kujerar zababben gwamnan jihar Bayelsa, David Lyon da kuma abokin tafiyarsa, Biobarakuma Degi-Eremienyo, wadanda suke ta shirye-shiryen karbar rantsuwar hayewa karagar mulkin jihar.

Tun kafin a rantsar da ni a aka bani gwarzon gwamnonin 2019 - David Lyon
Tun kafin a rantsar da ni a aka bani gwarzon gwamnonin 2019 - David Lyon
Asali: UGC

DUBA WANNAN: PDP ta yi martani kan ihun da 'yan Maiduguri suka yi wa Buhari

Alkalai biyar na kotun, wadanda suka samu shugabancin Mai shari'a Mary Peter-Odili, ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta janye shahadar hayewa kujerar jagorancin jihar da ta mikawa 'yan takarar jam'iyyar APC din a jihar, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Kotun kolin ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta da ta mika shahadar ga jam'iyya mai biye da ta APC din a yawan kuri'u a jihar idan aka duba sakamakon zaben da aka yi a ranar a 2019.

Duba da wannan kalami kuwa, jam'iyyar PDP ce za ta amshe wannan kujerar don ci gaba da mulkin jihar ta Bayelsa.

Mai shari'a Ejembi Ekwo, wanda ya karanto hukuncin kotun kolin, ya bada wannan umarnin ne bayan da aka bayyana rashin cancantar mataimakin David Lyon, Degi-Eremienyo a tsayawa takarar zaben.

Kotun ta jaddada hukuncin ranar 12 ga watan Nuwamba na 2019 wanda babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke na rashin cancantar abokin takarar Lyon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164