Rashin tsaro: Ba a adalci bane a dora wa Buhari laifi - Shettima

Rashin tsaro: Ba a adalci bane a dora wa Buhari laifi - Shettima

Sanata Kashim Shettima a ranar Alhamis ya ce rashin adalci ne a muzanta Shugaba Muhammadu Buhari saboda karuwar rashin tsaro a kasar.

Da ya ke zantawa da manema labarai bayan zaman majalisa a ranar Alhamis, ya ce binciko hanyoyin da za a warware matsalar kasar ya fi muhimmaci a maimakon dora wa shugaban kasar laifi.

Tsohon gwamnan na Borno ya ce, "Na yi imanin cewa yin maganganu domin burge mutane da kuma asasa matsalar ba zai warware matsalar ba. Ba zai yiwu kawai mu muzanta Buhari ba. Buhari ya yi iya kokarinsa kuma mun samu sauki daga 2015 zuwa 2017 kafin rikicin na Boko Haram ya sake tasowa.

"Binciko hanyoyin da za mu magance matsalolin mu ya fi muhimmaci a maimakon kokarin dora wa wani laifi.

DUBA WANNAN: PDP ta yi martani kan ihun da 'yan Maiduguri suka yi wa Buhari

Rashin tsaro: Ba a adalci bane a muzanta Buhari - Shettima
Rashin tsaro: Ba a adalci bane a muzanta Buhari - Shettima
Asali: Depositphotos

"Buhari ya taka rawar gani a arewa maso gabas. Ya taka muhimmiyar rawa wurin kafa Hukumar cigaban Arewa maso gabas. Idan har za mu fara nuna yatsa ga wadanda ke da laifi, ya kamata mu yi wa wannan tsohon adalci.

A ranar Laraba ne wasu mutane a Maiduguri babban birnin jihar Borno suka yi wa Shugaba Buhari ihu yayin da ya tafi yin jaje a jihar.

Shettima ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici inda ya ce akwai yiwuwar abinda mutanen Borno su ke tsammani daga wurin Buhari bai samu bane a game da yaki da ta'addanci.

"Mutane na tunanin Buhari yana da wani sandar tsafi ne. Ba shi da shi. Amma ina ganin wannan wani abu ne mai wucewa," in ji shi.

Dan majalisar ya ce mutanen Borno suka kaunar Buhari kuma suna goyon bayan gwamnatinsa da hukumomin tsaro.

Sai dai ya yi kira su hada kansu wuri guda domin magance kallubalen tsaron inda ya ce, "yaki da ta'addanci nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel