Jami'ar tarayya ta jihar Nasarawa za ta bawa Sheikh Dahiru Bauchi takardar digiri ta karramawa

Jami'ar tarayya ta jihar Nasarawa za ta bawa Sheikh Dahiru Bauchi takardar digiri ta karramawa

- Jami’ar tarayya ta Lafia da ke jihar Nasarawa za ta bada digirin karramawa ga babban malami Sheikh Dahiru Usman Bauchi

- Kamar yadda hukumar jami’ar ta sanar, hakan na daga cikin rukunin shagalin yayen dalibanta kashi na biyu, uku, hudu da biyar

- Jami’ar za ta karrama tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Al- Makura, saboda rawar da ya taka wajen tabbatar da habakar jami’ar

Jami’ar tarayya ta Lafia (FULafia), ta kammala shirye-shiryen bada digirin karramawa ga Sanata Umar Tanko Al-Makura, sanannen malamin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Ambasada Ahmed Gazali da kuma mashahurin mai arzikin nan na Kano, Abdulsamad Isiyaku Rabiu.

Hakazalika, mai martaba sarkin Lafia, Alhaji Isa Mustapha agwai, wanda ya rasu a 2019 za a karrama shi da digirin girmamawar, kamar yadda jaridar daily trust ta ruwaito.

Jami'ar tarayya ta jihar Nasarawa za ta bawa Sheikh Dahiru Bauchi takardar digiri ta karramawa
Jami'ar tarayya ta jihar Nasarawa za ta bawa Sheikh Dahiru Bauchi takardar digiri ta karramawa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Babbar magana: Wani mutumi ya daina ci da sha, ya ce yana so yaga yadda yunwa za ta kashe shi

A takardar da mai magana da yawun jami’ar, Abubakar Ibrahim ya fitar, ya ce girmamawar na daga cikin rukunin shagalin yayen daliban kashi na biyu, uku, hudu da na biyar na jami’ar wanda za a yi a ranar Asabar mai zuwa.

A takardar, an bayyana kalaman shugaban jami’ar Farfesa Mohammed Sanusi Liman na cewa, za a karrama tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Al-Makura ne saboda duba da irin kokarin da kuma gudumawar da ya bada wajen tabbatar da habakar jami’ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel