Ina mamakin akwai Boko Haram har yanzu - Buhari a Borno

Ina mamakin akwai Boko Haram har yanzu - Buhari a Borno

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma babbar birnin tarayya Abuja bayan ziyarar jajen da ta'azziyar da ya kai jihar kan kisan akalla mutane 30 a garin Auno, hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a ranar Lahadi.

Buhari ya dira Borno ne daga kasar Habasha inda ya kwashe kwanaki biyar a taron kasashen nahiyar Afrika.

Buhari ya bar Borno misalin karfe 4 bayan la'asar ba tare ziyartar garin Auno, inda aka kashe mutanen ba ko gaishe da wadanda suka jikkata kuma suke kwance asibiti ba.

Shugaban kasan ya bayyana cewa a fahimtar da ya yiwa al'adar kasar nan yana mamakin yadda Boko Haram ta rayu har zuwa yanzu.

Yace: "Saboda haka a fahimtar da na yiwa al'adarmu, ina mamakin yadda Boko Haram ta cigaba da kasancewa har yanzu."

Sabanin yadda yan Najeriya ke ganin harkar tsaro tana sake tabarbarewa kulli yaumin a kasar, shugaba Buhari ya bayyana cewa an samu cigaba a bangaren tsaro.

"Muna muku aiki a kasar nan. A matsayina da shugaban jami'an tsaro, ina tattaunawa da hukumomin tsaro kuma na yi imanin cew akwai cigaba a bangaren tsaro." Yace

Ina mamakin akwai Boko Haram har yanzu - Buhari a Borno
Ina mamakin akwai Boko Haram har yanzu - Buhari a Borno
Asali: Facebook

A bangaren guda, mun kawo muku rahoton cewa Mazauna Jiddari Polo a babbar birnin Borno, Maiduguri sun bayyana cewa sun ji harbe--harben bindiga da daren nan.

Hakan ya faru ne bayan ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari ya kai gain don jajintawa al'ummar jihar kan kisan mutane 30 a garin Auno ranar Lahadi 9 ga watan Febrairu, 2020.

Wasu yan ta'addan Boko Haram sun hallaka mutane 30 yayinda sukayi garkuwa da fasinjoji da dama a hanyar Maiduguri-Damaturu.

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa an kai wannan hari ne misalin karfe 9:50 na daren Lahadi a karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.

Bisa jawabin idanuwan shaida, yan ta'addan sun kona motoci 17 da dukiyoyin miliyoyin naira.

Wani mazauni, Ba'na Auni, wanda ya tsallake rijiya da baya yace yan ta'addan sun farwa fasinjojin da suka tsaya a garin Auno sakamakon kulle titin shiga Maiduguri da karfe 6 na yamma.

Yace: "Sun zo misalin karfe 9:50 na daren Lahadi kuma suka fara harbin mai uwa da wabi har muka arce cikin daji."

"Amma da muka dawo garin Auno da safen nan, mun samu an kashe fasinjoji tara amma mun gaza gane fuskokin biyar daga cikinsu ba saboda konewar da sukayi ,".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel