Magidanci ya lakada ma matarsa dan banzan duka har sai da ta ce ‘ga garinku’

Magidanci ya lakada ma matarsa dan banzan duka har sai da ta ce ‘ga garinku’

Wani magidanci dan shekara 42 da haihuwa, Ejiro Patrick ya lakada ma matarsa mugun duka har sai da ta daina numfashi a gidansu dake unguwar Tyomu, a wajen garin Makurdi na jahar Benuwe.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 12 ga watan Feburairu kamar yadda makwabtan ma’auratan suka tabbatar.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun kama buhun shinkafa cike da alburusai a jahar Zamfara

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa Ejiri dan asalin jahar Delta ne, kuma rikici ya kaure tsakaninsa da matarsa ne sakamakon zarginta da yake yi da coge na wasu kudade da aka biyata bayan ta sayar da wasu kayan dakinsu.

Shaidun sun bayyana cewa cikin fushi Ejiro ya dinga nausa ma matarsa naushi, kuma abinka da kosashshen mutum, zage karfinsa ya yi yana ta dukanta a bakin wani tafki, nan take ta yanke ta daina motsi.

Ganin haka yasa shaidun suka yi gaggawar daukanta tare da garzayawa da ita zuwa wani asibiti domin ceton rayuwarta, amma koda suka isa Asibitin tuni rai ya yi halinsa, ta shekara barzahu. Daga nan sai Ejiro ya yi zuru zuru, ido ya raina fata.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Benuwe, DSP Catherin Anene ta tabbatar da aukuwar lamarin, kuma ta ce tuni sun yi ram da magidancin, yana hannun Yansanda a yanzu.

Kaakakin ta ce Ejiro dan asalin jahar Delta ne, yayin da matarsa kuma yar asalin jahar Benuwe ce, kuma dalilin rikicin a cewar Yarsandan shi ne matar ta sayar da wasu kayayyakinsu, sai ta yi cogen N5000.

“Ejiro Patrick dake gida layin Gboko a unguwar KM14 Tyomu a garin Makurdi ya doki matarsa har lahira, daga bisani aka mika ta zuwa asibitin koyarwa na jami’ar jahar Benuwe inda aka tabbatar da mutuwarta. Matar ta yi ta zubar da jini ta hanci, a yanzu haka Ejiro yana hannun Yansanda, yayin da gawar ke can a dakin ajiyan gawarwaki.” Inji ta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel