Yanzu-yanzu: Daga fitan Buhari, An ji harbe-harbe a Maiduguri

Yanzu-yanzu: Daga fitan Buhari, An ji harbe-harbe a Maiduguri

Mazauna Jiddari Polo a babbar birnin Borno, Maiduguri sun bayyana cewa sun ji harbe--harben bindiga da daren nan.

Hakan ya faru ne bayan ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari ya kai gain don jajintawa al'ummar jihar kan kisan mutane 30 a garin Auno ranar Lahadi.

akalla mutane biyar sun jikkata yayinda Boko Haram sukayi kokarin shiga garin.

An tattaro cewa yan ta'addan sun shiga garin Maiduguri ne bayan Sallar Isha ta Addawari, unguwar Jiddari Polo inda suka harba roka da ya jikkata mutane 5.

Wani mazauni, Ali Maji Bukar, ya bayyana cewa na garzaya da wadanda suka raunata Asibitin jihar domin jinya.

"Bamu san abinda ya faru ba. Sai muka fara jin harbe-harbe a bayan gari da kuma hanyar Damboa." Yace

Sanda Bunu, wanda mazaunin Jiddari Polo ne ya ce bai ka yan ta'addan ba amma ya riga harsasai na yawo a sama.

"Jami'an tsaro sun zaburo da wuri kuma suka kawar da yan ta'addan amma har yanzu mutane na bakin hanya." Yace

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel