Ba tare da ziyartar Auno da aka kashe mutane ba, Buhari ya koma Abuja (Hotuna)

Ba tare da ziyartar Auno da aka kashe mutane ba, Buhari ya koma Abuja (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma babbar birnin tarayya Abuja bayan ziyarar jajen da ta'azziyar da ya kai jihar kan kisan akalla mutane 30 a garin Auno, hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a ranar Litinin.

Buhari ya koma birnin tarayyar ba tare da ziyartar wadanda suka rasa yan'uwansu da wadanda suka jikkata da ake jinya a Asibiti ba.

Alkaluma sun ce shugaban kasan ba jajintawa mutan Auno yayi ba saboda ko ziyartarsu bai yi ba, innama ya kaiwa mai martaba Shehun Borno gaisuwar ta'aziyya ne kan rashin yar uwarsa da yayi a ranar, 9 ga watan Febrairu, 2020.

Sun fadi hakan ne kan hujjan cewa ta yaya zai yi ikirarin jajintawa mutane ba tare da ziyartarsu da ganin irin ta'addancin da akayi musu ba bayan garin Auno bai wuce kilmita 5 da Maiduguri da ya je ba.

Buhari ya gana da manyan masu fada a ji na jihar Borno wanda ya hada da gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum; Shehu Borno, Mai martaba El-Kanemi da sauransu.

Misalin karfe 1 na rana gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya karbi bakuncin shugaban kasan tare da ministan walwala, Sadiya Umar Farouk da NSA, Babagana Munguno.

Daga nan ya garzaya fadar mai martaba Shehun Borno, Abubakar ElKanemi, sannan ya tafi gidan gwamnatin jihar domin jin abinci kafin ya fita daga jihar.

Ba tare da ziyartar Auno da aka kashe mutane ba, Buhari ya koma Abuja (Hotuna)
Ba tare da ziyartar Auno da aka kashe mutane ba, Buhari ya koma Abuja
Asali: Facebook

Ba tare da ziyartar Auno da aka kashe mutane ba, Buhari ya koma Abuja (Hotuna)
Ba tare da ziyartar Auno da aka kashe mutane ba, Buhari ya koma Abuja (Hotuna)
Asali: Facebook

Ba tare da ziyartar Auno da aka kashe mutane ba, Buhari ya koma Abuja (Hotuna)
Ba tare da ziyartar Auno da aka kashe mutane ba, Buhari ya koma Abuja (Hotuna)
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel