Super Eagles: Joseph Yobo ya zama Mataimakin Gernot Rohr

Super Eagles: Joseph Yobo ya zama Mataimakin Gernot Rohr

Mun samu labari cewa tsohon ‘Dan wasan Najeriya, Joseph Yobe, ya zama mataimakin mai horas da kungiyar ‘yan kwallon kasan watau Super Eagles.

Joseph Yobe ya karbi aikin tsohon kocin kungiyar nan ta Rangers, Imama Amapakabo, wanda ya kasance mai taimakawa Gent Rohr kafin wannan lokaci.

Tsohon ‘Dan bayan ya bugawa kungiyar Everton ta kasar Ingila na tsawon shekaru goma. Sannan kuma daga baya ya yi wasa a Fenerbahce da Norwich.

Yobo ya ajiye kwallo a Najeriya ne a shekarar 2014 bayan ya buga gasar cin kofin Duniya wanda aka yi a kasar Brazil. A lokacin Yobo ne ke rike da kambu.

Kafin nan ‘Dan wasan ya taimakawa Najeriya lashe gasar cin kofin kwallon kasa na Afrika a 2013. A wancan lokaci Stephen Keshi ne kocin Super Eagles.

KU KARANTA: Inter Milan ta karbi aron 'Dan wasan gaban Najeriya

Tsohon ‘Dan wasan mai shekaru 39 yanzu a Duniya ya bugawa Super Eagles a gasan AFCON na Nahiyar Afrika sau shida, inda ya yi nasarar daga kofin.

Yobe ya fara bugawa Najeriya ne a matakin U-20 a gasan da aka yi a 1999. Daga nan ne Super Eagles su ka fara kiran shi babban wasa a shekarar 2001.

Wani abin alfahari shi ne Yobo ya na cikin wadanda su ka taba bugawa Najeriya wasanni 100. Vincent Enyeama ne dayan wanda ya bar wannan tarihi.

A lokacin ya na Matashi shakaf, Yobo ya taka leda a kasar Beljika da Faransa, kafin zuwansa Ingila da Sifen. Kusan yanzu ne ya shiga harkar horaswa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel