Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, an yi shiru na minti 1 don wadanda aka kashe a harin Auno

Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, an yi shiru na minti 1 don wadanda aka kashe a harin Auno

- Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a yau Laraba, 12 ga watan Fabrairu

- A yayin taron an yi shiru na minti 1 ga wadanda aka kashe a harin Auno da kuma tsohon shugaban hafsan sojin ruwa, marigayi Vice Admiral Patrick Koshoni

- Babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya yi kira ga shirun na minti daya don karrama wadanda suka mutu

An gudanar da zaman majalisar zartarwa na mako a yau Laraba, 12 ga watan Fabrairu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya jagoranci zaman majalisar na yau.

A yayin zaman an yi shiru na minti guda domin karrama wadanda yan ta’addan Boko Haram suka kashe a ranar Litinin a Maiduguri, jahar Borno.

Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, an yi shiru na minti 1 ga wadanda aka kashe a harin Auno
Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, an yi shiru na minti 1 ga wadanda aka kashe a harin Auno
Asali: Facebook

An kuma yi shiru na minti guda don tsohon shugaban hafsan sojin ruwa, marigayi Vice Admiral Patrick Koshoni.

Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, an yi shiru na minti 1 ga wadanda aka kashe a harin Auno
Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, an yi shiru na minti 1 ga wadanda aka kashe a harin Auno
Asali: Facebook

Babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya yi kira ga shirun na minti daya don karrama wadanda suka mutu.

Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, an yi shiru na minti 1 ga wadanda aka kashe a harin Auno
Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, an yi shiru na minti 1 ga wadanda aka kashe a harin Auno
Asali: Twitter

A halin da ake ciki, mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo kasar bayan halartan taron AU na 33 a kasar Habasha.

Legit.ng ta rahoto cewa babban mai ba Shugaban kasa shawara kan kafofin watsa labarai, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 12 ga watan Fabrairu.

Ya ce Shugaba Buhari, ya taso daga Addis Ababa sannan a yanzun nan ya sauka a Maiduguri, babbar birnin jahar Borno.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Mutanen Borno sun yiwa Buhari ihun 'Bamayi' 'Bamaso' (Bidiyo)

Shugaban kasar ya kai ziyarar jaje ne ga gwamnati da mutanen jahar Borno biyo bayan mummunan lamarin da ya afku kwanan nan inda yan ta’addan Boko Haram suka kashe matafiya da dama.

Har ila yau mun ji cewa an yiwa shugaba Muhammadu Buhari ihu a Arewacin Najeriya. Faifan bidiyo dake yawo a kafafen ra'ayi da sada zumunta ya nuna yadda mutanen jihar Borno suke yiwa shugaban kasan ihun 'Bamayi' 'Bamaso' a ranar Laraba, 12 ga watan Febrairu, 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel