Tirkashi: An yankewa wani hukuncin kisa ta hanyar rataya, kan ya saci waya da kwamfuta

Tirkashi: An yankewa wani hukuncin kisa ta hanyar rataya, kan ya saci waya da kwamfuta

- Wata babbar kotun jiha da ke zama a Isabo da ke Abeokuta ta yankewa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya

- Kamar yadda lauyan gwamnatin ya sanar, alkali ya kama Olumide Akanbi ne da laifin fashi da makami

- A yayin da yaje fashin, wajen artabu da wanda suke yi wa fashin sai wayarsa ta fadi, wacce aka yi amfani da ita wajen kama shi tare da gurfanar da shi

Wata babbar kotun jiha da ke zama a Isabo, garin Abeokuta ta yankewa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya. A ranar Talata ne aka yanke wa wani Olumide Adekanbi hukuncin kisan sakamakon kama shi da aka yi da laifin fashi da makami.

Adekanbi da farko dai ya ki amsa laifuka biyun da ake zarginsa da su. An gano cewa ya aikata laifin ne a yankin Saraki-Adigbe da ke Abeokuta a 2016, kamar yadda jaridar Within Nigeria ta ruwaito.

Lauyan gwamnatin mai suna Owolabi Akinola ya sanar da kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne wajen karfe 4 na asuba a ranar.

Akinola ya sanar da kotun cewa, wanda ake zargin ya yi fashin waya kirar iPhone 6, laptop daya da kuma Ipad daya tare da abokan shi wadanda suka yi fashin tare.

KU KARANTA: To fa: Matsalar tsaro a kasar Libya na hanani bacci, ina matukar son na taimaka - Shugaba Buhari

An gano cewa, daga baya an kama su da kayayyakin don ya kai naurar mai kwakwalwa wani kauye da ke yankin Okelewo.

Wanda aka yi wa fashin mai suna Abowaba Salmon, ya sanar da kotun cewa Adekanbi ya buge shi da makami a yayin da yayi kokarin gudu.

Salmon ya kara da cewa, a lokacin da yake artabu da ‘yan fashin, wayar wanda aka yankewa hukuncin sai ta fadi kasa. Daga nan ne ya kaiwa ‘yan sanda kuma suka yi amfani da ita wajen gano inda yake har suka kama shi.

Bayan nan ne mai shari’a Balogun ya gamsu da shaidun tare da sakankacewa dan fashi ne. A take kuwa ya yanke mishi hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel