Gwamna Matawalle ya sha alwashin kwato naira biliyan 90 daga hannun Abdul’aziz Yari

Gwamna Matawalle ya sha alwashin kwato naira biliyan 90 daga hannun Abdul’aziz Yari

- Gwamna Bello Matawale na Jahar Zamfara ya lashi takobin cewa sai ya kwato kudi har naira biliyan 90 daga hannun tsohon gwamnan jahar , Abdul'aziz Yari

- Ana zargin Yari da karkatar da wadannan makudan kudi ta hanyar yin aragizon kwantaragi

- Matawalle ya ce zai aiwatar da shawarwarin da kwamitin bincike ya bayar ta hanyar tabbatar da ganin an hukunta duk mutumin da aka samu da laifi a jahar

Gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle, ya lashi takobin cewa sai ya kwato kudi har naira biliyan 90 daga hannun tsohon gwamnan jahar , Abdul'aziz Yari, wadanda ake zarginsa da karkatarwa ta hanyar yin aragizon kwantaragi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Matawalle, wanda ya bayyana haka a lokacin gabatar da wani rahoton kwarya-kwarya na kwamitin da aka dora wa alhakin tantance ayyyukan jahar, ya ce ba zai karaya ba har sai ya kwato dukkan kudin da aka karkatar da akalarsu daga jahar.

Gwamna Matawalle ya sha alwashin kwato naira biliyan 90 daga hannun Abdul’aziz Yari
Gwamna Matawalle ya sha alwashin kwato naira biliyan 90 daga hannun Abdul’aziz Yari
Asali: Facebook

“Zan aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar ta hanyar tabbatar da ganin an hukunta duk mutumin da aka samu da laifi,” in ji Matawalle.

Da farko dai mun ji cewa kwamitin bin diddigi domin tabbatar da aiyukan gwamnati a jihar Zamfara ya gano wasu motocin alfarma fiye da 100 da tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari, ya saya a kan kudi biliyan N8.4 ya raba ga 'yan uwa da abokansa.

A cikin wata sanarwa da ta fito ranar Talata daga ofishin Zailani Bappa, mai taimaka wa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, a kan harkokin sadarwa da yada labarai, ya bayyana cewa shugaban kwamitin, Ahmed Gusau, ne ya sanar da hakan a cikin rahoton 'somin tabi' da kwamitin ya mika wa gwamnan.

KU KARANTA KUMA: Kwankwaso da Abba gida-gida basu tarbi masoyinsu da ya yi tattaki daga Katsina ba

A cewar rahoton, tsohuwar gwamnati a karkashin Yari ta gaza nuna inda fiye da motoci 100, kwatankwacin kaso 66% na motocin da gwamnatin jihar ta mallaka, suke bayan karewar wa'adinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel