Ta bayyana: Gaskiyar dalilin da yasa Kwankwaso da Abba gida-gida basu tarbi masoyinsu da ya yi tattaki daga Katsina ba

Ta bayyana: Gaskiyar dalilin da yasa Kwankwaso da Abba gida-gida basu tarbi masoyinsu da ya yi tattaki daga Katsina ba

Dan takarar gwamna na babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a zaben jahar Kano da ya gabata, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi karin haske kan dalilin da yasa manyan yan Kwankwasiyya basu kasance a kasa ba don tarban Kwarad Aminu Aliyu, Tanko, wanda ya yi tattaki tun daga Katsina zuwa Kano domin yiwa Shugaban tafiyar jaje kan sakamakon hukuncin kotun koli.

Injiniya Abba ya ce dashi da uban tafiyar, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da sauran masu ruwa da tsaki na kungiyar duk suna a Abuja a wannan lokaci da Kwarad Aminu ya yi tattakin.

A wani jawabi da ke martani ga wani labara da kafar sadarwar yanar gizo ta wallafa wanda ya yi ikirarin cewa an bar dan Katsinar da ya yi tattaki a yashe a lokacin da ya isa Kano, dan takarar gwamnan ya bayyana cewa sabanin rahoton, mambobin akidar Kwankwasiya da sauran kungiyoyi sun yiwa Aminu kyakkyawar tarba.

Ta bayyana: Gaskiyar dalilin da yasa Kwankwaso da Abba gida-gida basu tarbi masoyinsu da ya yi tattaki daga Katsina ba
Ta bayyana: Gaskiyar dalilin da yasa Kwankwaso da Abba gida-gida basu tarbi masoyinsu da ya yi tattaki daga Katsina ba
Asali: Twitter

Jawabin wanda ke dauke da sa hannun babban sakataren labaran Abba, Malam Ibrahim Adam ya ce Kwamrad Aminu bai bayar da sanarwa kan kudirinsa na yin tattakin ba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“Za mu so jan hankalin jama’a kan gaskiyar cewa kafin wannan ziyarar da ake magana a kai, babu wani bayani da muka samu game da barinsa jahar Katsina wanda ya kamata ace an yi saboda tarin ayyukan da ke gaban shugabanninmu na gida da wajen jahar.

“Baya ga haka daga Sanata Rabiu Kwankwaso har mai girma Abba K. Yusuf da dukkanin masu ruwa da tsaki na Kwankwasiyya na a Abuja lokacin da mutumin ya iso Kano.

“Ya kuma kamata a san cewa duk da basu nan, mambobin Kwankwasiyya Akida da sauran kungiyoyi sun tarbe shi kamar yadda aka gani a shafukan zumunta, hakan na nuna karamci da son zumunci irin na mambobin tafiyar Kwankwasiyya,” in ji sanarwar.

Yayinda ake godiya ga karamcin Kwamrad Aminu, jawabin ya roki magoya bayan Kwankwasiyya a fadin duniya da su guji yin tattaki a cikin irin wannan lokaci da mai hatsari saoda halin da tsaro ke ciki a kasar da kuma yanayin dogon irin wannan zangon.

KU KARANTA KUMA: Rashin tarbiyya da kin girmama na gaba na daga cikin manyan matsalolin Kannywood – Tsohon Furodusa

“Muna duba izuwa haduwa dashi a lokacin da ya dace wanda za a shirya da zaran shugabanninmu sun dawo Kano,” in ji sanarwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel