Yan bindiga sun yi garkuwa da ayarin matafiya guda 10 a jahar Kogi

Yan bindiga sun yi garkuwa da ayarin matafiya guda 10 a jahar Kogi

Akalla matafiya guda 10 ne wasu gungun miyagu yan bindiga suka yi awon gaba dasu a kan babbar hanyar Obajana zuwa Abuja dake cikin garin Obajana na jahar Kogi, inji rahoton Punch.

Majiyarmu ta ruwaito har zuwa lokacin tattara rahoton babu wata masaniya game da sunayen fasinjojin motar, amma dan kasuwan dake da motar, Abdulganiyu Hakeem ya bayyana cewa motar ta tashi ne daga Ajowo Akoko.

KU KARANTA: Akwai tambayoyi dake bukatar amsoshi game da harin Auno – Sanata Kashim Shettima

Hakeem ya bayyana cewa: “Fasinjojin motar su 10 tare da direban duk suna hannun masu garkuwan a cikin kungurmin daji, daga cikin fasinjojin akwai wani dalibin kwalejin horas da lauyoyi dake Abuja.

“Mun samu labarin yan bindigan sun tattara kusan fasinjoji 30 daga motoci da dama da suka tare a kan hanyar, a cikin makon daya gabata.”

Sai dai yace rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindigan sun fara tuntubar iyalan wadanda suka kama, inda suke neman sai an biya kudin fansa kimanin naira dubu dari dari a kan kowanni mutum kafin su sake su, yayin da suka sanya N200,000 a matsayin kudin fansan direban.

A wani labarin kuma, rundunar Sojan kasa ta bayyana cewa ta ceto wasu dalibai guda uku daga hannun mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram bayan wata zazzafar gumurzu da musayar wuta da suka yi da juna a jahar Borno.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito babban kwamandan rundunar Soja dake yaki da yan ta’adda a yankin Arewa maso gabas, Manjo Janar Olusegun Adeniyi ne ya bayyana haka yayin da yake mika daliban uku ga iyayensu.

Adeniyi ya bayyana sunayen daliban kamar haka; Wommi Laja, Ammo Laja da kuma Kingi Laja, inda yace sun samu nasarar kubutar dasu ne bayan musayar wuta tsakanin yan ta’adda da wani hazikin Soja Laftanar Kanal Idris Yusuf, kwamandan Bataliyan Soja a Gubio.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel