Lawan da sauran 'yan majalisa sun ziyarci gidan Sanatan da ya mutu

Lawan da sauran 'yan majalisa sun ziyarci gidan Sanatan da ya mutu

Shugaban majalisar dattijan Najeriya, Ahmed Lawan, a ranar Talata ya jagoranci wakilcin manyan shugabannin majalisar dattijai don kai gaisuwar ta'aziyya ga iyalan Sanata Ignatius Longjang wanda ya rasu a ranar Lahadi.

A yayin ziyarar, Lawan ya bayyana marigayin da mutum mai son zaman lafiya kuma mai fatan samar da aiyukan jin dadi ga 'yan Najeriya.

Lawan da sauran 'yan majalisa sun ziyarci gidan Sanatan da ya mutu
Lawan da sauran 'yan majalisa sun ziyarci gidan Sanatan da ya mutu
Asali: Twitter

Mataimakin shugaban majalisar dattijan, Ovie Omo-Agege, shugaban majalisar, Yahaya Abdullahi, mataimakin bulaliyar majalisar, Sabi Abdullahi da kuma mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Philip Aduda na daga cikin shugabannin da suka hada tawagar.

A wata takarda da mai magana da yawun Lawan, Ola Awoniyi ya fitar, ya ce shugaban majalisar dattijan ba ya garin Abuja lokacin da abun ya faru amma ya dawo a ranar Talata. Daga filin jirgi ya zarce gidan marigayin tare da sanatocin da ke jiran shi.

Lawan da sauran 'yan majalisa sun ziyarci gidan Sanatan da ya mutu
Lawan da sauran 'yan majalisa sun ziyarci gidan Sanatan da ya mutu
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An gano motocin alfarma 100 na biliyoyin Naira da tsohon gwamna Yari ya karkatar

Lawan, a madadin majalisar ya jajantawa matar marigayin sanatan, Mrs Maureen Longjang, diyarsa, Mikang Longjang da kuma sauran iyalansa.

"Marigayi Sanata Longjang ya kasance mai tabbatar da zaman lafiya. Mutum mai halaye nagari tare da biyayya. Ya mayar da hankali wajen aiyukan majalisar. Ya gina gadoji. Ya so komai ya tafi dai-dai. Kuma a matsayinsa na babba a majalisar, kowa na mutunta shi tare da bashi girma. Wannan babban rashi ne garemu baki daya." in ji shi.

Lawan da sauran 'yan majalisa sun ziyarci gidan Sanatan da ya mutu
Lawan da sauran 'yan majalisa sun ziyarci gidan Sanatan da ya mutu
Asali: Twitter

"Zamu ci gaba da aiki tare da iyalansa tare da sanatoci biyu na jihar Filato din don ganin mun shirya masa bikin birneshi yadda ya dace," Lawan ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel