Jerin kamfanonin Najeriya 6 da CBN ta bawa lasisin shigo da 'Kindirmo' daga ketare

Jerin kamfanonin Najeriya 6 da CBN ta bawa lasisin shigo da 'Kindirmo' daga ketare

Babban bankin kasa (CBN) ta bawa wasu kamfanonin cikin gida guda shidda lasisin shigo da madarar shanu (Kindirmo) daga kasashen waje.

CBN ta bawa Kamfanonin izinin ne ranar Talata a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun Ozoemena Nnaji, darektan kasuwanci da musaya.

Jerin kamfanonin da CBN ta ambata sune kamar haka; Friesland Campina WAMCO Nigeria, Chi Limited, TG Arla Dairy Products Limited, Promasidor Nigeria Limited, Nestle Nigeria PLC da Integrated Dairies Limited.

Darektan ya bayyana cewa bawa kamfanonin lasisi yana bisa tsarin kudirin gwamnati na habaka samar da Madara a cikin kasa da kuma sauran wasu abubuwan da ake sarrafa su da Madara.

Jerin kamfanonin Najeriya 6 da CBN ta bawa lasisin shigo da 'Kindirmo' daga ketare
Babban bankin kasa (CBN)
Asali: UGC

A cikin sanarwar, wacce ta fara aiki nan take, CBN ta bayyana cewa kamfanonin 6 ne kadai suke da lasisi daga gwamnati domin shigo da Kindirmo daga kasashen ketare.

DUBA WANNAN: Abinda Buhari ya fada a kan Boko Haram bayan sun kai sabon hari a Borno

CBN ta ce bata bawa wani Kamfani takardar shahada mai alamar 'M' ba bayan kamfanonin data ambata a sama ba. Takardar shahada ta 'M' ta zama wajibi a cikin takardun da kamfanonin shigo da kayan abinci ke bukata kafin su shigo da wani kaya cikin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel