Abinda muka tattauna da Dame Patience a Villa yayin ganawarmu - Aisha Buhari

Abinda muka tattauna da Dame Patience a Villa yayin ganawarmu - Aisha Buhari

Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta gana da Dame Patience, matar tsohon shugaban kasa a fadar shugaban kasa.

A sanarwar da ta fitar a shafinta na dandalin sada zumunta (Tuwita) ranar Talata, Aisha Buhari ta bayyana cewa sun gana ne domin tattauna harkokin da suka shafi cigaban mata a fadin kasa.

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana cewa tattaunawarsu ta tsaya ne a kan harkokin da suka shafi bunkasa cigaban mata a fadin kasa, musamman batun ilimin 'ya'ya mata da shigar mata harkokin siyasa a kowanne mataki.

"A jiya (Litinin) ne na karbi bakuncin uwargidn tsohon shugaban kasa, Dame Patience, a fadar gwamnati.

"Mun tattauna a kan kokarin ganin mata sun shiga harkokin siyasa domin dama wa dasu a cikin harkokin gudanar da gwamnati a kowanne mataki.

Abinda muka tattauna da Dame Patience a Villa yayin ganawarmu - Aisha Buhari
Dame Patience da Aisha Buhari
Asali: Facebook

"Sannan mun tattauna a kan ilimin 'ya'ya mata da kuma gidauniyar da ta kafa mai taken 'Women for Change'," a cewar Aisha Buhari.

Ta bayyana cewa akwai bukatar matan tsofin shugabannin kasar nan su hada kansu tare da tuntunbar juna domin tattauna hanyoyin inganta rayuwar 'ya'ya mata da yara a cikin al'umma.

"Na saurari labarin yadda ta sha gwagwarmaya a lokacin da suke kan mulki da muka irin fahimtarta a kan abubuwa da dama da suka shafi rayuwar mata da kananan yara a cikin al'umma," a cewarta.

DUBA WANNAN: Abinda Buhari ya fada a kan Boko Haram bayan sun kai sabon hari a Borno

Aisha Buhari ta bayyana matukar jin dadi da godiya ga Dame Patience bisa ziyarar da ta kai mata.

"Na ji dadin kasancewa tare da ita kuma ina fatan zamu cigaba da samun lokaci irin wannan," kamar yadda ta wallafa a shafinta na Tuwita.

A makon jiya ne Aisha Buhari ta karbi bakuncin Turai Yar'adua, uwargidan tsohon shugaban kasa, Marigayi Umar Musa Yar'adua a fadar gwamnati, Asovilla.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel