Sanata Elisha Abbo ya siyi timatirin N100 kan N50k a hannun yar shekara 4 da ke talla a Adamawa

Sanata Elisha Abbo ya siyi timatirin N100 kan N50k a hannun yar shekara 4 da ke talla a Adamawa

- An gano Sanata Elisha Abbo na aikata aikin alkhairi kan wata yar karamar Yarinya

- Sanatan ya bayyana cewa ya siyi timatir na N100 daga wajen yarinyar yar shekara hudu da ke talks a kan Naira dubu 50

- Abbo ya kuma bayyana cewa zai dauki nauyin yarinyar domin ta yi karatu a kyauta

Sanatan Najeriya, Elisha Abbo ya je shafinsa na sadarwa don sanar da cewar zai taimaka wa Wata Yarinya a Loko, jahar Adamawa.

Sanatan ya yi sanarwar a shafinsa na Facebook.

Ya yi bayanin cewa yana a hanyarsa ta zuwa Yola domin yiwa yan kasuwa jajen asarar shaguna da dukiyoyinsu da suka yi sanadiyar gobara lokacin da ya yi karo da wata yarinya yar shekara hudu tana tallar timatir.

Ya ce ya zub da hawaye kan yarinyar mai shekara hudu. Sai yace ya tambaye ta cewar zai siyi timatir wanda tace N100 ne.

Sanata Elisha Abbo ya siyi timatirin N100 kan N50k a hannun yar shekara 4 da ke talla a Adamawa
Sanata Elisha Abbo ya siyi timatirin N100 kan N50k a hannun yar shekara 4 da ke talla a Adamawa
Asali: Facebook

Abbo ya yi bayanin cewa ya siyi timatir din kan Naira dubu 50. Ya ce ya mayar mata da timatir din cewa ta ba magaifiyarta ta yi mata abinci dashi.

Sanatan ya kuma bayyana cewa ya yiwa mahaifinta alkawarin cewa zai dauki nauyin karatunta.

Sanata Elisha Abbo ya siyi timatirin N100 kan N50k a hannun yar shekara 4 da ke talla a Adamawa

A gefe guda kuma, mun ji labarin wata mai suna Dele karamar yarinya ‘yar makaranta wacce aka ga tana amfani da hasken ATM din bankin FCMB wajen yin aikinta na makaranta. Mazauniyar jihar Ondo ce da kakarta, kuma hotunanta sun jawo cece-kuce a kafofin sada zumuntar zamani.

A yayin da karamar yarinyar ke amfani da hasken ATM din, wani ma’aboci amfani da kafar sada zumuntar zamani ta twitter ya ganta tare da daukar hotonta. Ya wallafa hoton wanda ya yadu a kafar sada zumuntar.

Bayan wannan hoton ya kai ga hukumar bankin ne, sai suka nemi a nemo musu inda zasu ga Dele yadda zasu dau nauyin karatunta, kamar yadda jaridar Within Nigeria ta wallafa.

Rahotanni da yawa sun tabbatar da cewa Dele na zama ne tare da kakarta kuma an gano su. A halin yanzu tana zuwa wata makaranta ne mai suna Hope of Glory Academy a Ondo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel