Likitocin ‘Ya ‘yan mutum daya da kowa ya ke ta magana a kansu

Likitocin ‘Ya ‘yan mutum daya da kowa ya ke ta magana a kansu

Wata Baiwar Allah ta wallafa hotunan Mata biyar wanda ta bayyana cewa ‘Yanuwan juna ne, da su ka yi tarayya a wajen aiki.

Duka wadannan Mata da su ka dauki hoto, Likitoci ne kamar yadda za a fahimta daga yanayin kayan da su ke dauke da shi.

A kasashe irin Najeriya, an saba ganin Likitoci a matsayin Maza, inda ake barin Mata da irinsu aikin Ungon-zoma da sauransu.

Yanzu abubuwa sun fara canzawa, wadannan Mata cikin kayan asibiti da hotonsu ya ke yawo, duk sun fito ne daga gida daya.

Kamar yadda mu ka samu labari daga wajen wanda ta wallafa hoton; daga cikin Matan akwai kwararriyar Likitar kwakwalwa.

KU KARANTA: 87% na Talakawan Najeriya su na Yankin Arewa - Bankin Duniya

Daya kuma Likitar aikin mata ce, yayin da guda kuma ta zama Likitan Iyali. Daya daga cikinsu kuma Likitar al’umma ce.

Ta karshen su kuwa ta kware ne a fannin yin aikin fida na canza yanayin jikin mutane. Dukansu mutum daya ya haife su.

A Najeriya dai ana fama da karancin Likitocin kwakwalwa da kuma Likitocin da ke fidar da ke canza kamannin mutane.

Atiku Abubakar ya yi magana game da wadannan mata, inda ya ce duk wanda ya ba Mace ilmi, ya ilmantar da al'umma

Dazu kun ji labari cewa tsohon shugaban Amurka, Barack Obama, ya kan yi kuka idan ‘Ya ‘yansa su ka samu wata daukaka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng