Yanzu-yanzu: Bam ya tashi a jihar Edo

Yanzu-yanzu: Bam ya tashi a jihar Edo

Bam ya tashi a gidan sakataren jam'iyyar All Progressives Congress na Edo Mr. Lawrence Okah misalin karfe 12:30 na dare. The Nation ta ruwaito.

Bam din ya fashi wani bangaren gidan kuma ya haka rami a kasa.

Babu rayuwar da ya salwanta a wannan hari.

Jami'an hukumar yan sandan kawar da bama-bamai sun dira gidan misalin karfe 8 na safe domin dauke sauran Bam daya da bai tashi ba.

Manyan jigogin jam'iyyar APC a jihar irinsu Osagie Ize-Iyamu, da Dakta Pius Odubu sun dira gidan domin jajantawa sakataren.

Zamu kawo muku cikakken rahoton...

Asali: Legit.ng

Online view pixel