Miyetti Allah: Za ayi amfani da Amotekun ne wajen fatattakar Kabilu daga Kudu

Miyetti Allah: Za ayi amfani da Amotekun ne wajen fatattakar Kabilu daga Kudu

Shugabannin kungiyar Miyetti Allah, sun gabatar da dalilan da su ka sa ba su goyon bayan Jami’an tsaron Amotekun da aka kirkiro a daukacin jihohin Kudu maso Yamma.

Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta reshen jihar Bauchi ta bakin shugabanta, ta yi magana game da wannan Dakaru da aka kirkiro da sunan inganta tsaro.

Alhaji Sadiq Ahmed, a madadin Miyetti Allah Kautal Hore ya ke cewa manufar Amotekun ita ce a kori kabilar Fulani daga Yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Sadiq Ahmed ya kuma bayyana cewa Jami’an tsaron na Amotekun ba su da hurumin yin aiki a wadannan Jihohi na Najeriya domin doka ba ta tanadi zamansu ba.

Miyetti Allah Kautal Hore ta bakin Ahmed ta yarda cewa ana fama da matsalar rashin tsaro a Najeriya, sai dai a na ta ganin, canzawa jami’an tsaro zani ne mafita.

KU KARANTA: Gwamnan Borno ya yi wa Sojoji kaca-kaca kan harin Auno

Miyetti Allah: Za ayi amfani da Amotekun ne wajen fatattakar Kabilu daga Kudu
Miyetti Allah Kautal Hore ba za ta yarda da aikin Amotekun ba
Asali: Twitter

Ahmed ya ke cewa abin da ake bukata shi ne gwamnati ta yi wa daukacin Malaman tsaro garambawul, ba wai kowane yanki su fito da Dakarun tsaronsu ba.

Kamar yadda Jaridar Vanguards ta rahoto, wannan shiri na Amotekun da aka kirkiro ba zai kai ko ina ba, domin dokar Najeriya bai san da zamanshi ba inji Ahmed.

“Akwai wani mai wata tababa cewa makusudin kafa wannan shiri shi ne kawai a shafe kabilar mu daga Kudu maso Yammacin Najeriya?” kungiyar ta tambaya.

“Harkar tsaro ya rataya ne a kan gwamnatin tarayya. Duk wasu Dakarun da aka kirkira dabam da jami’an tsaron kasa, kishiya ne aka yi wanda sam bai halatta ba.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng