Uwargidar Obama ta bada labarin yadda Mijinta ya barka kuka wajen biki yaye ‘Diyarsu

Uwargidar Obama ta bada labarin yadda Mijinta ya barka kuka wajen biki yaye ‘Diyarsu

Tsohuwar Uwargidar kasar Amurka, Michelle Obama, ta fito ta bada labarin yadda Mijinta ya saba barkewa da kuka game da lamarin ‘Ya ‘yansa ‘Yan mata da ya ke da su.

A wajen wata hira da aka yi da Michelle Obama, ta bayyana cewa abu kadan ya kan iya taba zuciyar Mijinta, musamman idan ‘Ya ‘yansa su ka ci wata nasara a rayuwa.

Michelle Obama ta yi wannan bayani baro-baro ne a lokacin da ta yi hura da Oprah Winfrey. Misis Michelle ta ce Mai gidanta ya saba yin wani irin ‘mummunan kuka’ a fili.

A cewar Obama, tsohon shugaban kasar Amurkan ya na boye hawayensa ne a karkashin bakaken tabarau da ya ke makawa a idanunsa. Wannan ya sa ba a iya ganewa.

Lokacin da Barack Obama da Mai dakinsa su ka ajiye ‘Ya ‘yansu a Makaranta, sai ya barke da kuka yayin da yake kallon ‘Yan matan na shi su ke tafiya zuwa ajinsu.

KU KARANTA: Shehin Najeriya ya yi wa Obama tayin karbar Musulunci

Uwargidar Obama ta bada labarin yadda Mijinta ya barka kuka wajen biki yaye ‘Diyarsu
Dodewa da bakin tabarau ke hana a ga kukan Obama inji Michelle
Asali: Getty Images

Har lokacin da Malia ta ke bikin kammala jami’a, Mahaifin na ta wanda ya taba rike kasar da ta fi kowace karfi a Duniya, ya sharba kuka da karfi kuma a bainar jama’a.

“Mu ka yi kokarin shiga da ita cikin mota ta yadda ba za ta fara kuka ba, sai ni ma in dauka, daga nan Barack ya kama, haka mu ke yi kamar kananan yara.” Inji Michelle.

Obama ya yi kuka ne a lokacin da ya fara kallon bidiyon bikin yaye ‘Daliban wanda ‘Diyarsa ta ke cikinsu. “Kun san Obama ya na wani irin kuka ne da karfin tsiya.”

Michelle da Barack sun yi aure ne tun 1992, kuma sun samu ‘Ya ‘ya biyu; Malia da Sasha. Duk da irin soyayyar da ke tsakaninsu, Michelle ta ce a kan samu sabani.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel