Abubuwa 6 da Allah ya yiwa Musulmai ni'ima da su da ya sanya jikinsu baya wari

Abubuwa 6 da Allah ya yiwa Musulmai ni'ima da su da ya sanya jikinsu baya wari

Musulunci addini ne na zaman lafiya, kuma addini ne mai tsafta. Ba zai yiwu kana Musulmi ba kuma baka da tsafta. Da wuya kaga Musulmi namiji ko mace suna warin jiki ko kuma na baki

Hakan ya samo asali saboda irin tsaftar da addinin Musulunci ya gindaya a kan kowanne Musulmi. Ga jerin abubuwa guda shida da suka sanya jikin Musulmai ba ya wari:

1. Tsarki bayan anyi fitsari

Musulmi na amfani da ruwa suyi tsarki a duk lokacin da suka yi fitsari. Saboda duk lokacin da wannan fitsari ya taba jikin mutum ko kayan shi idan yayi sallah ba za ta karbu ba, saboda babu tsarki a tare da mutum.

2. Tsarki bayan anyi bayan gida

Musulmai basa amfani da takarda ko wani abu su goge bayan gida idan sun gama, a matsayinka na Musulmi, ana bukatar mutum yayi amfani da ruwa wajen wanke bayan gida idan ya kammala, domin hakane hanya daya ta tsarkake kanshi.

3. Salloli guda biyar a rana

Sallah sau biyar a rana ta zama wajibi ga kowanne Musulmi. Sannan kuma sallah ba ta karbuwa idan babu alwala. Alwala ita ce hanyar da mutum zai tsarkake kanshi kafin ya gaida Ubangiji.

KU KARANTA: Wanda ya lashe gasar mafi lalaci a duniya, ya tura abokinshi ya karbo mishi kyautar da aka bashi

4. Wankan Janaba

Tilas ne Musulmi yayi wankan janaba a duk lokacin da ya sadu da iyalin shi. Idan har ka sadu da iyali kuma baka yi wankan janaba ba, Musulunci ya hana ka ka kusanci Masallaci ko Al-Qur’ani mai girma.

5. Aske gashin gaba dana hammata

Ana bukatar Musulmi ya dinga aske gabanshi da kuma hammatar shi, domin tsaftace kanshi daga warin jiki.

6. Wanke baki kafin ayi karatun Qur’ani

Musulmai suna wanke bakinsu kafin su karanta Al-Qur’ani mai girma, saboda shi littafi ne mai tsarki, saboda haka dole sai mutum ya tsarkake kanshi kafin ya karanta shi. Amma wannan ba wai farilla bane.

Da wadannan abubuwa da Musulmai suke yi yau da kullum, da wuya kaga jikin Musulmi ko bakinshi yana yin wari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel