Daga karshe: Jonathan ya bayyana dalilin sauke Farida Waziri

Daga karshe: Jonathan ya bayyana dalilin sauke Farida Waziri

- Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kara magana a kan Farida Waziri, tsohuwar shugabar EFCC

- A cikin kwanakin nan ne Farida Waziri ta bayyana cewa Jonathan ya sauketa ne saboda wata harkalla man fetur

- Farida Waziri ce dai tsohuwar shugabar hukumar yaki da rashawa da hana yi wa arzikin kasa zagon kasa, wato EFCC

A cikin sabon littafinta ne tsohuwar shugabar hukumar yaki da rashawa ta EFCC, Farida Waziri, tayi ikirarin cewa Jonathan ya tsigeta daga kujerarta a wancan lokacin ne saboda bincikar wasu masu damfarar man fetur da take.

Waziri ta sanar da hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da ita a 2017, wanda hakan ta sa mai magana da yawun Jonathan, Ikechukwu Eze ya gaggauta yi mata martani.

Hakazalika, Eze ya musanta ikirarin tsohuwar shugabar EFCC din tare da ganin rashin kyautawar kalamanta.

Daga karshe: Jonathan ya bayyana dalilin sauke Farida Waziri
Daga karshe: Jonathan ya bayyana dalilin sauke Farida Waziri
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: 2023: Cancanta za mu duba ba yanki ba wurin zaben dan takarar shugaban kasa - Sule Lamido

“Tsigeta yana da nasaba ne da ra’ayin Najeriya da kuma duniya wanda ya kamata Goodluck ya barshi a matsayin sirri. Akwai bukatar a sani, a yayin da ake mu’amala da ra’ayin kasa, kwazon aiki na wannan ofishin ake dubawa kuma ba za a taba ba ra’ayin shugaban fifiko ba.” Takardar ta ce.

“Wadanda zasu cigaba da magana a kan hakan, su sani cewa wannan aikin kasa ne ba sarauta ba, kuma ‘yan kasa ne suka amince mata.” Takardar ta kara cewa.

A wani labari na daban kuwa, shugabannin jam’iyyar PDP sun yanke hukuncin tunkarar Jonathan a kan ya hanzarta shiga tare da jagorantar rikicin da jam’iyyar ke fama da shi.

“Jonathan na daya daga cikin manyan jam’iyya da ake mutuntawa kuma ake so har yanzu. Hakan ne yasa muka yanke shawarar rokarsa don ya zo yayi sasanci tare da hada kanmu. Muna bukatarsa a yayin da 2023 ke gabatowa. Zamu tunkaresa tare da bashi shugabanci,” daya daga cikin manyan jam’iyyar ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel