EFCC: Adoke ya fadawa kotu zai fi son ya zauna a gidan yarin Kuje

EFCC: Adoke ya fadawa kotu zai fi son ya zauna a gidan yarin Kuje

A Ranar Litinin, 10 ga Watan Fubrairun 2020, tsohon Ministan shari’an Najeriya, Mohammed Adoke SAN, ya bayyana cewa ya fi sha’awar a tsare shi a gidan yarin Kuje.

Tsohon Ministan ya nuna cewa zai fi son ya zauna a kurkukun da ke Garin Kuje, a madadin hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa ta rike sa.

Bello Adoke ya yi wannan jawabi ne ta bakin babban Lauyan da ke kare sa a gaban Alkali, Cif Mike Ozekhome SAN, bayan an cigaba da shari’a a babban kotun tarayya.

Ana ta faman shari’a tsakanin hukumar EFCC da Mohammed Bello Adoke SAN da kuma wani Aliyu Abubakar ne a wani babban kotun tarayya da ke zama a Birnin Abuja.

Ana zargin Bello Adoke da Aliyu Abubakar da laifin biyan wasu kudi da su ka kai Naira miliyan 300 (a kudin Najeriya) cikin wani asusu a 2013, wanda hakan ya sabawa doka.

KU KARANTA: EFCC za ta iya cigaba da rike Adoke domin bincike - Kotu

EFCC: Adoke ya fadawa kotu zai fi son ya zauna a gidan yarin Kuje
Lauyan Adoke ya ce tsohon Ministan ya na fama da rashin lafiya
Asali: UGC

Mike Ozekhome ya yi magana game da belin wadanda ya ke karewa, inda ya fadawa Alkali cewa EFCC ta kinkimo tsohon Ministan ne daga wani asibitin gwamnati da ke Abuja.

Lauya Bala Sanga wanda ya tsayawa EFCC a shari’ar ya bukaci hukumar ta cigaba da tsare Bello Adoke, har zuwa lokacin da Alkali zai yanke hukunci game da batun belinsa.

Yayin da Mike Ozekhome ya ke rokon Alkali ya sassauta sharudan belin wanda ake tuhuma, ya nuna cewa wanda ake zargin zai fi so ya zauna a cikin gidan yarin da ke Kuje.

Ozekhome ya ce: “Wanda ake tuhuma, da kansa ya ga dama ya dawo kasar nan. Ba tserewa ya yi ba. Mun gabatar da takardu da su ka nuna cewa karatu ya tafi yi a kasar waje.”

“Mai shari’a abin da doka ta ce shi ne ‘ka zo ka tsayawa shari’a’. Kamar yadda ka ke gani, wanda ake tuhuma ya haura shekaru 60 a Duniya, tsufa ta fara kama shi.” Inji Lauyan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel