Yanzu-yanzu: Wani Sanatan APC daga jihar Plateau ya mutu
Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa Sanata Ignicious Longjan mai wakiltar mazabar Plateau ta kudu a majalisar dattawa, ya rigamu gidan gaskiya.
Sanatan ya mutu ne a wani Asibitin kasar Turkiyya
Mai maga da yawun Sanatan, Mr Wulime Goyit, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a garin Jos.
Gabanin zama Sanata, Ignacious Longjan, ya kasance mataimakin gwamnan jihar Plateau karkashin tsohon gwamna, Jonah Jang.
Saurari cikakken rahoton...
Asali: Legit.ng