Yanzu-yanzu: Bayan shekaru 5, an bude hanyar Maiduguri-Dikwa

Yanzu-yanzu: Bayan shekaru 5, an bude hanyar Maiduguri-Dikwa

A ranar Lahadi, gwamnatin jihar Borno ta bude titin Maiduguri zuwa Dikwa, bayan shekaru biyar da rufeta sakamakon rikicin Boko Haram da ya addabi Arewa maso gabashin Najeriya, musamman jihar Borno.

NAN ta ruwaito cewa an rufe hanyar mai tsawon kilomita 86 ne a shekarar 2015 yayinda rikicin Boko Haram yayi kamari.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, tare da tiyata kwamandan , Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Olusegun Adeniyi da GOC na 7 Div, , Operation Lafiya Dole, Birgediya Janar, Abdul Khalifa , suka bude hanyar.

KARANTA WANNAN: Yanzu-yanzu: Wani Sanatan APC daga jihar Plateau ya mutu

Gwamna Zulum a jawabinsa ya jinjinawa hukumar Sojin Najeriya kan nasarar da suke samu wajen dakile yan ta'addan Boko Haram da suka addabi al'umma.

Ya ce bude hanyar zai raya tattalin arzikin al'ummar yankin musamman masunta.

Ya ce direbobi za su iya tafiya a hanyar cikin kwanciyar hankali ba tare da rakiyar Sojoji ba saboda komai ya yi sauki yanzu.

Zulum ya ce gwamnatin jihar na tattaunawa da Sojoji kan yadda matafiya za su ita tafiya a Ngala da Kala Balge ba tare da rakiyar Sojin ba.

Yace: "Kowa a Borno ya san abubuwan da ke faruwa a manyan tituna. Wannan ba sabon abu bane kuma ba wanke kowa muka zo yi nan ba."

"Dokar Najeriya ba ta hana mutane safarar kayayyakinsu cikin jiha ba, saboda haka, ba zai yiwu ku ce dk direban da ya dauki kaya sai ya biya kudi ba."

"Ta yaya mutum zai dauki ruwa ko Tumatur amma a ce sai ya biya N19,000 ga motoci masu tayoyi shida."

Bayan haka, gwamnan jihar ya baiwa hukumar Sojojin Mafa kyautar motocin sintiri 6 domin karfafa ayyukansu da kuma kokarin da gwamnatin tarayya keyi wajen kawo karshen ta'addanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel