Sabon salo: Mambobin majalisa zasu ke tafiya hutun minti 15 domin mike kafa yayin zaman majalisa

Sabon salo: Mambobin majalisa zasu ke tafiya hutun minti 15 domin mike kafa yayin zaman majalisa

'Yan majalisar wakilai sun kirkiro da tafiya hutun mintoci 15 a duk zaman majalisar don "mike kafafu", jaridar Daily Trust ta gano. Sun ce suna bukatar mike kafafunsj bayan dogon zama a zauren majalisar.

Mai magana da yawun majalisar, Benjamin Kali dan jam'iyyar APC daga jihar Abia, ya ce wannan hutun zai ba Musulmai damar zuwa salla yayin da wasu zasu samu abun motsa baki.

"A likitance, ana bada shawarar cewa a guji dogon zama waje daya. Hakan baya kawo ingancin lafiya. Yana shafar zagayen jini a jiki. A don haka ne ake shawartar jama'a da su guji zaman waje daya," ya ce.

"Kun san cewa jama'ar da ke majalisar wakilannan ba matasa bane. Kadan daga ciki ne ke da kuruciya. Duk da haka kuma akwai bukatar mutum ya zagaya na dan lokaci. A basirar wannan gida shine aka kirkiro da mintoci 15 na mike kafafa." Ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel